logo

HAUSA

An sako daliban Kuriga da aka sace a farkon Maris a tsakiyar Nijeriya

2024-03-24 20:46:22 CMG Hausa

Uba Sani, gwamnan jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya, ya bayyana a yau Lahadi 24 ga wata cewa, an sako daliban firamare da na sakandare da aka yi garkuwa da su a jihar a farkon wannan wata.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a shafin sada zumunta. Ya kuma godewa kusoshin siyasa ciki har da shugaban kasar Bola Tinubu, da ma sojoji bisa kokarin da suka yi, amma bai bayyana adadin daliban da aka sako ba, da takamaiman yadda aka sako su, da kuma halin da masu garkuwan suke ciki.

A ranar 7 ga watan Maris ne wasu ‘yan bindiga suka kutsa cikin makarantun firamare da sakandare na Kuriga da ke cikin garin Kuriga, a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna, inda suka yi garkuwa da dimbin dalibai. Rahotanni daga kafafen yada labarai na kasar sun bayyana cewa, shugaban makarantar sakandaren Kuriga, Sani Abdullahi wanda ya yi nasarar kubuta daga hannun ‘yan bindiga, ya ce akalla dalibai 287 daga makarantun biyu ne suka bace, wadanda suka hada da daliban makarantar sakandare 187 da na firamare kimanin 100. (Mai fassara: Bilkisu Xin)