logo

HAUSA

Adadin jarin waje da kasar Sin ta yi amfani da su a zahiri a shekarar 2023 ya kai matsayi na uku a tarihinta

2024-03-24 16:39:48 CMG Hausa

Bayanin da kwamitin raya kasa da yin kwaskwarima na kasar Sin ya fidda, ya nuna cewa, a shekarar 2023, adadin jarin waje da kasar Sin ta yi amfani da su a zahiri ya kai matsayin gaba a tarihin kasar. Bayan da kasar Sin ta fara bude kofa ga waje da yin gyare-gyare a gida, adadin jarin waje da take amfani da su a zahiri yana ci gaba da karuwa, lamarin da ya sa, a halin yanzu, kasar Sin ta zama mihimmiyar kasa da kamfanonin kasashen duniya suka fi zuba jari.