logo

HAUSA

WHO ta yi kira da a hada hannu domin ganin bayan tarin fuka a Afrika

2024-03-24 17:03:05 CMG Hausa

Hukumar lafiya ta duniya (WHO), ta ce ya kamata kasashen Afrika su hada hannu tare da zuba jari kan manyan shirye-shiryen da za su kai ga ganin bayan cutar tarin fuka baki daya, zuwa shekarar 2030.

Babbar jami’ar hukumar a nahiyar Afrika Matshidido Moeti ce ta bayyana haka a jiya Asabar, jajibirin ranar yaki da tarin fuka da ake gudanarwa a duk ranar 24 ga watan Maris din kowacce shekara.

A cewarta, abu ne mai yuwuwa a iya rage tasirin annobar sosai a nahiyar da zarar gwamnatoci da masana’antu da abokan hulda masu bada gudunmuwa sun zuba jari ga sabbin shirye shiryen ganowa da rigakafi da jinyar cutar.

Ta ce tarin fuka na ci gaba da kasancewa kwayar cuta ta biyu mai yaduwa mafi kisa a nahiyar Afrika, inda ta zarce kwayoyin cutar kanjamau na HIV da AIDS. Ta ce a shekarar 2022, kimanin mutane miliyan 2.5 ne suka kamu da cutar a nahiyar, wato kwatankwacin kamuwar mutum 1 cikin kowacce dakika 13. 

Matshidiso Moeti ta kara da cewa, musayar ilimi da ingantattun dabarun takaita yaduwar cutar tarin fuka yadda ya kamata da gaggauta gano ta da ma hadin gwiwa a yankuna, na da muhimmanci wajen tabbatar da cutar ba ta ci gaba da zama barazana ga lafiyar al’umma ba a Afrika.

Bugu da kari, ta yaba da ci gaban da aka samu wajen yaki da cutar a Afrika, inda aka samu raguwar mace-mace sanadiyyar cutar da kaso 38 a tsakanin shekarar 2015 da 2022, yayin da a lokaci guda, aka samu raguwar sabbin masu kamuwa da ita da kaso 23 cikin 100. (Fa’iza Mustapha)