logo

HAUSA

Hawayen munafurci

2024-03-24 21:58:10 CMG Hausa

Daga Lubabatu Lei

Yanzu haka musulmi a sassan duniya na cikin watan Ramadan mai tsarki. A daidai wannan lokaci, sakataren harkokin wajen kasar Amurka Antony Blinken ya fitar da sanarwa a kwanan baya, inda ya yi wa al’ummar musulmi gaisuwar watan Ramadan, tare da bayyana cewa, “musulmai ‘yan kabilar Uygur a jihar Xinjiang ta kasar Sin, da ‘yan kabilar Rohingya na kasashen Myanmar da Bangladesh, da Palesdinawa na zirin Gaza, suna fama da rikice-rikice da wahala.”

Ba wani abu da ya fi “hawayen munafurci” dacewa da siffanta wannan sanarwar da Mr.Blinken ya bayar, sabo da tun bayan barkewar rikici a tsakanin Palasdinu da Isra’ila a wannan karo, duk da tsanantar yanayin jin kai a zirin Gaza, Amurka ta yi ta rura wutar rikicin, a sa’i da kuma take “kuka”.

Kasancewarta babbar kawar Isra’ila da ma kasar da ta fi samar mata makamai, tun bayan barkewar rikicin, Amurka ta yi ta kara samar da gudummawar soja ga Isra’ila. Bisa rahoton da kafofin yada labarai na kasar ta Amurka suka bayar, an ce, ya zuwa yanzu, gwamnatin Biden ta sayar da makaman soja fiye da sau 100 a asirce ga Isra’ila,  ciki har da makamai sama da dubu 10, matakin da ya sa masana’antun samar da makamai da ma masu ruwa da tsaki na kasar suka ci kazamar riba. Duk da mummunan yanayin jin kai da ake ciki a Gaza, sau hudu Amurka ta na jefa kuri’ar nuna rashin amincewa da kudurin da aka gabatar ga kwamitin sulhu na MDD dangane da tsagaita bude wuta a zirin Gaza. Sai kuma a kwanakin baya, ita Amurka din ta gabatar da wani daftarin kuduri ga kwamitin sulhu dangane da batun tsagaita bude wuta a zirin Gaza, amma a maimakon ta ce a tsagaita bude wuta nan da nan, sai ta gindaya sharuda ga tsagaita bude wuta, wanda ya saba wa daidaiton da akasarin mambobin kwamitin sulhun suka cimma, don haka, ba a kai ga zartas da shi ba.

Amma ga shi yanzu, Mr.Blinken ya fara damuwa da yanayin da Palasdinawa a zirin Gaza ke ciki, shin da gaske ne ya damu? Ba shakka ba haka ba ne, sabo da a kafin ya ambaci Pasdinawa, Mr.Blinken ya fara ne da ambaton “musulmai ‘yan kabilar Uygur a jihar Xinjiang ta kasar Sin”, lallai ainihin burinsa ke nan ya fake da sunan kulawa da yanayin da Palasdinawa a zirin Gaza ke ciki da ma hakkin musulmi don dakile kasar Sin ta hanyar amfani da wai yanayin da ‘yan kabilar Uygur ke ciki a jihar Xinjiang.

Amma karya fure take ba ta ‘ya’ya, duk wadanda suka taba zuwa jihar Xinjiang, ciki har da masana na kasashen yamma da ‘yan jarida da jakadu na kasashen musulmi dake kasar Sin, sun gano cewa, ana samun zaman lafiya da bunkasuwar tattalin arziki da zaman jituwa a tsakanin mabiya addinai daban daban a yankin Xinjiang na kasar Sin, kuma ana tabbatar da hakkin dan Adam na daukacin jama’a, ciki har da ‘yan kabilar Uygur. A hakika, babu rikici a yankin Xinjiang na kasar Sin, zirin Gaza ne ke fuskantar rikice-rikice. Haka kuma musulmai na yankin Xinjiang ba sa fama da yunwa ko kisa, amma miliyoyin musulmai na zirin Gaza suna fama da wadannan matsaloli.

Sama da kwanaki 160 ke nan tun bayan barkewar rikici a tsakanin Palasdinu da Isra’ila, wanda ya sa fararen hula sama da dubu 32 suka rasa rayukansu, baya ga miliyoyin dake fama da yunwa. Kamata ya yi Amurka ta daina wasan siyasa da yanayin jin kai na zirin Gaza. Abin da ya kamata ta yi shi ne ta dauki hakikanan matakai na ceton rayukan musulmai a Gaza, a maimakon ta fitar da sanarwa maras ma’ana.(Mai Zane:Mustapha Bulama)