logo

HAUSA

An kama wasu makaman yaki a Nijar da ake shirin shiga da su kasar Cote d’Ivoire

2024-03-23 14:45:58 CMG Hausa

A kasar Nijar, jami’an tsaro na rundunar Niyya da ke sintiri a jihar Tera, yankin Tillabery sun kama wata motar dakon kaya dauke da manyan makaman yaki da aka boye karkashin buhuhuwan hatsi. Bayan kama direban motar da yaransa, an gudanar da binciken motar ciki da waje.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto. 

A ranar jiya Juma’a 22 ga watan Maris, mujallar jami’an tsaro ta ranar 17 zuwa 20 ga watan Maris din shekarar 2024, ta sanar ta hanyar gidan talabijin na kasa RTN da gano wadannan makaman yaki.

A cewar wannan mujallar, makaman sun hada da harsasai fiye da 1140, nakiyoyin fasa tankokin yaki, da wasu kananan bindigogi, takardar taswirar Parc de W da ke cikin yankin Tillabery, na’urar kallo daga nesa guda 6, hullar yaki guda 2, kakin soja, fasfo, da sauran kayayyakin da suka hada tutar kasar Amurka guda 3, lasisin mota na kasar Amurka, da katin banki guda 2 duk da sunan wasu mutane biyu ’yan kasar Amurka.

Mujallar ta kara da cewa, bisa binciken farko da aka gudanar, shaidu sun nuna kasar Amurka, tare da aza ayar tambaya kan salsalar wadannan kayayyakin yaki da kuma inda za’a kai wadannan makaman yaki.

Labarin ya karkare da cewa, bincike na ci gaba da zurfafa domin tantance masu hannu da kuma bangarorin da suke cikin wannan al’amari.

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.