logo

HAUSA

Shugaban gwamnatin sojan janhuriyar Nijar ya gana da jakadan Sin

2024-03-23 20:27:55 CMG Hausa

Jiya Juma'a, shugaban gwamnatin sojan janhuriyar Nijar Abdourahamane Tchiani ya gana da jakadan kasar Sin a Nijar Jiang Feng, inda bangarorin 2 suka yi musayar ra'ayi dangane da huldar dake tsakanin kasashen 2, gami da hadin gwiwar da ake yi tsakaninsu.

Yayin ganawar, jakada Jiang na kasar Sin ya ce, kasarsa ta riga ta mika gayyata ga bangaren Nijar, don halartar taron dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka da zai gudana a kasar Sin nan da wasu watanni. Ya ce ana sa ran ganin haduwar dimbin shugabannin kasashen Afirka da na kasar Sin a birnin Beijing na kasar Sin, inda za su tattauna batun karfafa hadin gwiwar kasashensu a nan gaba. Jakadan ya kara da cewa, kasar Sin na son yin amfani da wannan dama, wajen habaka hadin kai da mu'ammala tare da bangaren Nijar, da kara zurfafa huldar dake tsakanin kasashen 2.

A nasa bangare kuwa, shugaba Tchiani, ya jinjinawa hulda mai kyau dake tsakanin kasarsa da kasar ta Sin. A cewarsa, Nijar ta dora matukar muhimmanci kan sabon taron dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka dake tafe, kana tana da imini kan cewa taron zai taimakawa, wajen karfafa hadin kai da zumunta tsakanin kasashen Afirka da kasar Sin, tare da samar da nasarori.

Shugaban ya kara da cewa, yana fatan ganin kasashen Nijar da Sin su habaka hadin gwiwarsu zuwa sabbin fannoni, karkashin tsarin dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka, ta yadda za a samar da dimbin sakamako da zai amfani karin al'ummar Nijar. (Bello Wang)