logo

HAUSA

Shugaban kwamitin ECOWAS: Sin ta taka muhimmiyar rawa ga ci gaban yankunan yammacin Afirka

2024-03-23 20:06:58 CMG Hausa

Jakadan Sin a Najeriya Cui Jianchun, ya gana da shugaban kwamitin ECOWAS Omar Alieu Touray a jiya Jumma’a, inda suka yi musayar ra’ayoyi game da zurfafa dangantakar abokantaka, da kuma hadin gwiwa tsakanin Sin da ECOWAS.

Yayin ganawar tasu Touray ya bayyana cewa, Sin ta dade tana taka muhimmiyar rawa a harkokin kasa da kasa, ta ba da babbar gudummawa ga ci gaban yankunan yammacin Afirka. Ya ce kwamitin ECOWAS ya dora muhimmanci kan dangantaka dake tsakaninsa da Sin, yana kuma fatan kara zurfafa hadin gwiwa a fannoni daban daban tare da bangaren Sin, ta yadda za a inganta ci gaba lami lafiya a yankunan yammacin Afirka.

A nasa bangare kuwa, jakada Cui ya bayyana cewa, bangaren Sin ya dora muhimmanci kan gudummawar ECOWAS, ga karfafa dungulewar yankin, da kiyaye zaman lafiyar yankin, da kuma inganta ci gaban zamantakewar al’umma da tattalin arziki na kasashen mambobin ECOWAS da sauransu. Har ila yau, bangaren Sin zai ci gaba da karfafa mu’ammala tsakaninsa da ECOWAS a bangarori daban daban, da ba da tallafin gina ofishin hedkwatar kungiyar, da kuma inganta bangarorin biyu samun sabon sakamakon hadin gwiwa. (Safiyah Ma)