logo

HAUSA

Nijar ta bude iyakar ta da Najeriya

2024-03-22 21:03:39 CMG Hausa

A yau Juma’a ne gwamnatin soji a janhuriyar Nijar, ta sanar da bude kan iyakar kasar da tarayyar Najeriya.

Manazarta na cewa, matakin zai bayar da damar komawa hada hadar cinikayya a tsakanin yankunan kan iyakar kasashen biyu, mai tsawon kilomita 1,500, wadda aka rufe tun ranar 30 ga watan Yulin bara, bayan da majalissar ceton kasa ta sojojin Nijar ko CNSP, ta kifar da gwamnatin farar hula a ranar 26 ga watan na Yulin bara. (Saminu Alhassan)