logo

HAUSA

Kasar Sin ta bukaci a hada hannu wajen shawo kan matsalar jin kai a Syria

2024-03-22 14:30:53 CMG Hausa

Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Geng Shuang, ya bukaci kasa da kasa su hada hannu wajen shawo kan matsalar jin kai a Syria, da samar da mafita a siyasance ga matsalar kasar.

Geng Shuang ya kara kira ga kasa da kasa su kara yawan tallafin jin kai da suke ba Syria da ba da isassun kudade ba tare da kayyade su ba, domin tallafawa kammaluwar ayyukan farfado da kasar.

Ya kuma jaddada cewa, ya kamata kasa da kasa su girmama matakan da kasar ta samar ta kuma jagoranta da kanta da karfafa tattaunawa da tuntubar juna, domin samar da mafitar da za ta karbu ga dukkan bangarori.

Geng Shuang ya ce tun bayan barkewar wannan zagaye na rikicin Palasdinu da Isra’ila, Isra’ila ta kaddamar da hare-hare ta sama kan wurare daban-daban na Syria, daga yankunan da ta mamaye na tuddan Golan da iyakarta da Lebanon da ake kira Blue Line, lamarin da ya keta cikakken ‘yancin Syria da ikon da take da shi kan yankunanta.

A cewarsa, kasar Sin ta damu matuka. Duk da ta’azzarar rikici tsakanin Palasdinu da Isra’ila, ya kamata dukkan bangarori su kai zuciya nesa, su kaucewa ta’azzarar yanayin da kara karfi daga juna da kuma kaucewa bazuwar rikicin. Haka kuma, ya kamata manyan kasashen dake wajen yankin, su taka muhimmiyar rawa wajen ganin an shawo kan rikicin. (Fa’iza Mustapha)