logo

HAUSA

Najeriya ta lashe zinare na ajin tseren maza hudu na mita 100 a gasar wasannin Afirka karo na 13

2024-03-22 10:35:30 CMG Hausa

Najeriya ta lashe lambar zinare na ajin tseren maza hudu na mita 100 na gudun ba da sanda a gasar wasannin Afrika karo na 13 da ake gudanarwa a Accra, babban birnin Ghana.

A ranar da ta yi kama da ranar daukakar kasarsu, 'yan wasan Najeriya na ajin tseren maza hudu sun kammala tseren cikin dakika 38.41 inda suka kwace lambar zinare daga hannun Ghana, wadda ta lashe a Morocco a shekarar 2019.

Ghana ce ta zo ta biyu da dakika 38.43 ta samu azurfa, yayin da kasar Laberiya ta yammacin Afirka ta samu tagulla, inda ta kare a cikin dakika 38.73.

A wannan daren ne kuma ’yan wasan Najeriya na ajin tseren mata hudu na mita 100 na gudun ba da sanda su ma suka lashe lambar zinare a wannan filin wasan. (Yahaya)