logo

HAUSA

Jakadan Sin dake Najeriya ya gana da ministan wajen kasar

2024-03-22 19:54:40 CMG Hausa

Jakadan Sin dake Najeriya Cui Jianchun, ya gana da ministan harkokin wajen kasar Yusuf Tuggar a jiya Alhamis, inda suka yi musayar ra’ayoyi game da zurfafa dangantakar Sin da Najeriya, da kuma inganta hadin gwiwar kasashen biyu.

Jakada Cui ya bayyana cewa, hadin gwiwar Sin da Najeriya na ci gaba da bunkasa lami lafiya. Kana a shekarun baya bayan nan, an zurfafa hadin gwiwa a fannonin bunkasa ababen more rayuwa, da karfin wutar lantarki, da raya masana’antu da sauransu tsakanin kasashen biyu, wadanda suka wadata dangantakar dake tsakaninsu.

Tuggar ya bayyana cewa, Sin ta samu gagarumin sakamakon ci gaba, ta kuma taka rawar gani sosai a harkokin kasa da kasa. Kaza lika bangaren Najeriya na fatan ci gaba da karfafa amincewar juna ta fuskar siyasa, da hadin gwiwa mai inganci tare da bangaren Sin, ta yadda za a inganta samun sabon sakamako na bunkasuwar dangantakar kasashen biyu. (Safiyah Ma)