logo

HAUSA

Babban taron MDD ya yi kira da a samar da tsarin AI mai aminci don samun ci gaba mai dorewa

2024-03-22 13:47:55 CMG Hausa

Taron Majalisar Dinkin Duniya a jiya Alhamis ya zartas da wani kuduri na inganta tsarin fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam wato AI mai aminci, da tsaro don samun ci gaba mai dorewa.

Kudurin ya jaddada bukatar samar da tsarin fasahar AI bisa amintaccen ma’auni da tsaro don habaka sauye-sauye na dijital, ba tare da kawo cikas ga damar samun moriyar tsarin bisa daidaito ba, don samun ci gaba mai dorewa da magance kalubalolin da duniya ke fuskanta, musamman ga kasashe masu tasowa.

Ya kuma karfafa gwiwar kasashe mambobin MDD, kuma ya yi kira ga masu ruwa da tsaki daga dukkan yankuna da kasashe da su habaka da tallafawa ka'idoji da hanyoyin gudanar da tsare-tsare masu alaka da aminci, da tsaro na tsarin fasahar AI wanda zai ba da gudummawa ga samun kyakkyawan yanayin muhalli a dukkan matakai.

Kudurin ya kara jaddada cewa dole ne a mutunta, kiyaye da kuma tallata hakkin dan adam da ’yancin dan adam a duk tsawon wanzuwar tsarin fasahar AI. (Mohammed Yahaya)