logo

HAUSA

Kasar Sin na kara amfani da fasahar AI wajen kirkiro sabbin mutum-mutumin inji

2024-03-22 16:43:30 CMG Hausa

A halin yanzu, kasar Sin na kara amfani da fasahar AI wato fasahar kwaikwayon tunanin bil’adama, wajen kirkiro sabbin mutum-mutumin inji, al’amarin da ya kara basira gami da kwarewar mutum-mutumin inji, wajen yin karatu da gudanar da ayyuka masu sarkakiya.

Wasu kwararrun ma’aikata daga lardin Zhejiang dake gabashin kasar Sin sun kirkiro wani sabon nau’in mutum-mutumin inji mai siffar jiki irin na dan Adam, wanda ke da kwarewa wajen gudanar da ayyuka iri daban-daban. An saka na’ura mai kwakwalwa dake amfani da fasahar AI a cikin wannan mutum-mutumin inji, wanda kuma ke kunshe da fasahar sarrafa gabobin jikin dan Adam ta zamani.