logo

HAUSA

Gwamnatin jihar Jigawa ta tabbatar da cewa kaso 50 ne kawai na adadin filin noman dake jihar ake iya nomawa

2024-03-22 09:23:22 CMG Hausa

Gwamnan jihar Jigawa dake arewa maso yammacin Najeriya Dr. Umar Namadi ya tabbatar da cewa, har yanzu jihar ba ta iya noma  fiye da kaso hamsin na filayen noman da ake da su a fadin jihar baki daya.

Gwamnan ya tabbatar da hakan ne ranar Alhamis 21 ga wata lokacin da ya karbi bakuncin ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na tarayyar Najeriya Alhaji Muhammed Idris a gidan gwamnatin jihar. Ya ce, kaso 90 na murabba’in filayen dake jihar ta Jigawa suna da albarkar noma sosai.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Gwamnan na jihar ta Jigawa ya ci gaba da cewa, tuni gwamnatin jihar ta yi nisa wajen aiwatar da manufofin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta fuskar sha’anin noma domin wadata kasa da abinci.

“Muna da fadin kasa da ya kai a kalla murabba’in sikwaya mita dubu 22 kuma daga cikin wannan adadi kaso 80 wurare ne dake da dausayin noma, kama daga na damina zuwa na rani wanda za a iya aikatawa a kowanne lokaci na watannin shekara. Amma mai girma minista a zancen nan da nake yi kaso 50 ne kawai na wadannan filaye ake yin noma a cikinsu.”

A jawabinsa ministan yada labaran na tarayyar Najeriya Alhaji Muhammed Idris ya ce, gwamnatin tarayyar tana alfahari matuka da jihar Jigawa ta fuskar noman abinci. Lamarin da ya danganta da himma da kuma kwazon da gwamnan jihar ke nunawa a wannan fage.

“A yau jihar Jigawa ita ce fitila dake haskawa Najeriya baki daya, hanyar da za a bi a kai ga gaci a kan harkokin da suka shafi sha’anin noma.”

Daga karshe ministan yada labaran a madadin gwamnatin tarayya ya yi kira ga gwamnonin jihohin kasar da su himmatu wajen alkinta albarkatun da jihohinsu suke da su domin rage wahalhalun da al’ummar kasa ke ciki ta fuskoki daban daban. (Garba Abdullahi Bagwai)