logo

HAUSA

Hedkwatar CDC ta Afirka ta samu yabo a matsayin babban sakamakon hadin gwiwar BRI

2024-03-22 10:03:17 CMG Hausa

Tawagar malamai da jami’ai na kasar Sin a ranar Alhamis sun yabi hedkwatar cibiyar yaki da cututtuka ta Afirka (Afirka CDC) da kasar Sin ta gina a kasar Habasha, a matsayin wata babbar alama ta hadin gwaiwa tsakanin Sin da Afirka karkashin shirin shawarar “Ziri Daya da Hanya Danya” (BRI).

Wannan ya zo ne a daidai lokacin da tawagar kasar Sin da ta kunshi shehun malamai daga jami’ar horar da malamai ta Beijing, da jami’an gwamnatin kasar Sin, da sauran masu ruwa da tsaki, suka ziyarci hedkwatar CDC ta Afirka da ke yankin kudancin Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha.

A watan Janairun 2023 ne aka kaddamar da hedkwatar CDC ta Afirka da kasar Sin ta gina, wadda ake daukarta a matsayin babban aikin hadin gwiwar kiwon lafiyar jama’a na Sin da Afirka. A watan Nuwamba na shekarar 2023, Cibiyar CDC ta Afirka ta kuma kaddamar da wani dakin gwaje-gwajen bincike da kasar Sin ta ba da taimakon ginawa a hedkwatarta.

Yayin da hukumar ta Afirka CDC ta yi bikin cika shekaru bakwai da kafuwa kwanan nan, babban daraktan hukumar ta Afrika CDC Jean Kaseya, shi ma ya yaba da goyon bayan da kasar Sin ke bayarwa wajen baiwa hukumar damar gudanar da aikinta ta hanyar horaswa don inganta aiki da taimakon fasaha.

Da yake magana da kamfanin dillancin labarai na Xinhua kwanan nan, Kaseya ya ce, aikin hedkwatar zai taka muhimmiyar rawa wajen inganta lafiyar al'umma a Afirka. (Mohammed Yahaya)