logo

HAUSA

Kyakkyawar huldar Sin da Austriliya ta dace da muradun al’ummun kasashen biyu

2024-03-22 11:43:27 CGTN HAUSA

 

“Daga batun dabbar Panda zuwa harajin kwastam, da dukkan abubuwan da ministan harkokin wajen Sin da ta Austriliya suka tattaunawa cikin sahihanci”, kafar yada labarai ta Ausriliya wato “Australian Associated Press” ta yi tsokaci kan tattaunawa karo na 7 kan diplomsiyya da manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Austriliya. Wanda ke nuni da kyautatuwar  huldar kasashen biyu. Mambam ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya ziyarci Austriliya a watan Maris da muke ciki, wanda ya kasance matakin ingiza farfadowar huldar kasashen biyu.

Wani manazarci ya bayyana cewa, Austriliya ta iya samun moriya tare da Sin, muddin ta canja tsarin da take a kai, na bin bayan Amurka da hana bunkasuwar Sin daga tushe, da kuma gaggauta daukar karin matakan kyautata huldar kasashen biyu.

A halin yanzu dai, kasar Sin na hanzarta aiwatar da shirin zamanintar da al’ummarta daga dukkan fannoni, matakin da ya samar da mabambanta damammaki ga kasashen duniya ciki har da Austriliya.

Tsohon firaministan kasar Austriliya Paul John Keating ya bayyana yayin ganawarsa da wakilan Sin cewa, “ina da kwarin gwiwa matuka kan makomar huldar kasashen biyu,” a cewarsa, Sin da Austriliya kasashe masu karfi ne a yankin Asiya da Pacific, tarihi ya nuna cewa ba su da matsala kuma manyan muradunsu ba su sabawa da juna. A halin yanzu kuma, kamata ya yi a zabi sabuwar hanyar raya huldarsu don samun ci gaba tare. Kamar yadda Sin take nanata cewa, in har ana son tabbatar da akidar huldar kasashen biyu, to ya zama dole a samu bunkasuwa mai karko kuma mai dorewa zuwa nan gaba. Wannan ne zai biya muradun jama’ar kasashen biyu, shi ne kuma buri na kasashen dake wannan yanki. (Amina Xu)