logo

HAUSA

Najeriya za ta yi amfani da madatsar ruwan Shiroro a jihar Niger wajen samar da wuta ta amfani da hasken rana

2024-03-21 12:15:31 CMG Hausa

 

Mataimakin shugaban tarayyar Najeriya Sanata Kashim Shettima ya tabbatar da cewa, gwamnatin kasar ba za ta taba yin wani abu da zai kawo cikas ga shirinta na sauyawa zuwa amfani da makamashi mai tsafta wajen samar da wuta a kasar ba.

Ya tabbatar da hakan ne yayin bikin sanya hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa tsakanin kamfanin samar da wutan lantarki na North South da hukumar kula da zuba jari ta Najeriya a kan batun samar da kamfanin wutan lantarki ta amfani da hasken rana a madatsar ruwa ta Shiroro dake jihar Niger, inda za a yi amfani da fasahar zamani wajen shimfida farantan wutar Sola a kan ruwa.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Sanata Kashim Shettima ya bayyana yarjejeniyar a matsayin wani mahimmin mataki da zai bunkasa shirin sauya tsarin samar da wuta a kasar ta hanyar rungumar hanyoyin amfani da makamashi mai tsafta.

Mataimakin shugaban kasar ya ce, gwamnatin tarayyar Najeriya bisa jagorancin shugaba Bola Ahmed Tinubu za ta ci gaba da marawa duk wani shirin da zai kai ga bunkasuwar tattalin arzikin da wadatuwar makamashin da zai taimaka wajen kare muhalli.

Ya ce babu shakka samar da tashar wutar mai karfin Megawat 20 ta amfani da haske rana a madatsar ruwan ta Shiroro wani babban ci gaba ne ga kasa baki daya.

“Wannan yajejeniyar hadin gwiwa tsakanin kamfanoni da aka sanyawa hannu a yau ya tabbatar da kudirin da muke da shi da rungumar tsarin amfani da makamashi mai tsafta kuma wanda ake sabuntawa, a matsayinmu na kasa matakin da muka dauka shi ne mu fadada hanyoyinmu ta samar da makamashi tare da rage gurbatacciyar iska da kuma tabbatar da makoma mai dorewa ga ’yan baya.”

Shi dai aikin samar da tashar wutar sola mai karfin Megawatt 20 a Shiroro ta jihar Niger, wani bangare ne na shirin samar da wuta ta amfani da hasken rana mai karfin megawatt 300 wanda ke samun tallafin bankin masana’antu na tarayyar Najeriya da hadin gwiwa da sauran hukumomi da kamfanonin lura da sha’anin wutar lantarki na kasar. (Garba Abdullahi Bagwai)