Sin na maraba da Australiya da ta tsara manufofinta da kanta
2024-03-21 14:26:24 CMG Hausa
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, a yau Alhamis ya bayyana cewa, kasar Sin tana maraba da kasar Australiya, kawar Amurka, kuma abokiyar huldar Sin, bugu da kari kasa mai cikakken iko, ta aiwatar da manufofinta bisa dogaro da murandunta na asali.
Wang ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da tsohon firaminstan Australiya Paul Keating.
Wang ya kuma yaba da dauwwamammiyar kulawa da goyon bayan da Keating yake bayarwa ga bunkasuwar dangantakar dake tsakanin Sin da Australiya, yana mai cewa, hanyar zamanantarwa ta kasar Sin babbar gudummawa ce ga ci gaban wayewar dan Adam, kuma a shirye kasar Sin take ta more damar samun ci gaba tare da sauran kasashe ciki har da Australiya.
A nasa bangaren, Keating ya bayyana cewa, kasar Sin tana da tattalin arziki mai karfi wanda ke fadada damar ci gaba, wanda kuma ba shi da wata barazana ga sauran kasashen duniya, kuma yana taimakawa wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin. Da yake kara karfafa yakininsa game da ci gaban da kasar Sin wanda ba za a iya dakatarwa ba, Keating ya bayyana kwarin gwiwa kan hasashen kyakkyawar dangantakar Australia da Sin. (Yahaya)