logo

HAUSA

Kasar Sin ta ci gaba da samar da taimakon jin kai ga yankin Gaza

2024-03-21 11:18:01 CMG Hausa

Bayanin da ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Masar ya fidda, ya nuna cewa, gwamnatin kasar Sin tana ci gaba da samar da gudummawar da ake bukata ga Falasdinu domin sassauta matsalar jin kai a yankin Gaza. Ya zuwa yanzu, ban da taimakon kudi, kasar Sin ta kuma samar da taimakon jin kai na gaggawa sau biyu ga yankin Gaza ta kasar Masar, wadanda suka hada da abinci, da magunguna da kuma kayayyakin jinya.

Yanzu ana cikin watan Ramadan, kasar Sin na gaggauta aikin samar da hatsi da abinci ga yankin Gaza. A ranar 28 ga watan Maris, za a isar da shinkafa da kasar Sin ta samar wa Falasdinu a tashar jiragen ruwa ta Said dake kasar Masar, sa’an nan, za a yi jigilar su zuwa yankin Gaza ta tashar Rafah. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)