logo

HAUSA

Wasan kwallon kwando ta gargajiya na inganta rayuwar matan kananan kabilu a kudu maso yammacin Sin

2024-03-21 21:11:36 CMG Hausa

Matan kananan kabilu dake gundumomin Qiandongnan Miao da Dong masu cin gashin kai dake karkashin lardin Guizhou na kudu maso yammacin kasar Sin, sun fara gudanar da wasan kwallon kwando da salo irin na kwallon kafa, inda ake baiwa ‘yan wasa damar yin guje-guje da kwallo, cikin filin wasa ba tare da busa wasu laifuka da aka saba yi cikin wasan a hukumance ba.

Mazauna wadannan yankuna na kiran wannan nau’i na kwallon kwando da "Kwallon kwando ta Gu-Ma", kasancewar tana gudana ne tsakanin mata da suka yi aure a wasu wurare da ba yankunan su na asali ba.

A cewar Shi Fang, jami’a a sashen lura da wasanni ta kauyen Leishan na gundumar Qiandongnan,"Gu-Ma" na nufin mace da ta yi aure a wajen yankin ta. Wasa ne da ya samo asali daga kauyen Paili na al’ummar Miao tun shekaru 20 da suka gabata. Gundumar Qiandongnan na da sama da kabilu 33, ana kuma gudanar da bukukuwan gargajiya sama da 200 a duk shekara a gundumar.

Bisa al’ada, matan yankin na buga gasar kwallon kwando domin shagalin wadannan bukukuwa, amma kasancewar da daman su ba su da kwarewa ta wasan kwallon kwando, sai suka rika kago na su dokokin gargajiya na gudanar da wasan.

Tsakanin ranar 8 zuwa 10 ga watan nan na Maris ne aka gudanar da gasar "Gu-Ma", a kauyen Xijiang na gundumar Leishan karkashin gundumar Qiandongnan, gasar da ta samu halartar kungiyoyin yankin 19.

Wata matashiya ‘yar shekaru 22 dake karatu a sashen ilimin motsa jiki a kwaleji Wang Yuxin, tana buga kwallon kwando da aka saba da ita. Bayan ta kalli bidiyon wasan kwallon kwando na "Gu-Ma" a shafin TikTok, ta kuma shiga wasan a karon farko, ta ce wasan na da ban sha’awa.

Kaza lika, ita ma wata mai yawon bude ido mai suna Liu, ta halarci wasan kwallon kwandon ta karkara, kuma yayin da take nadar wasan da wayar hannun ta, ta bayyana cewa, iyalin ta sun nishadantu da yadda wasan yake gudana cikin annashuwa.

Liu ta ce "A baya ba mu taba jin labarin wannan wasa na sada zumunta ba. Yana da ban sha’awa. ‘yan wasan suna da son juna da hadin kai. Wasan kwallon kwando na "Gu-Ma" yana inganta rayuwar matan kananan kabilu, yana samar musu da farin ciki, tare da ba su damammaki na haduwa da juna da kulla abota.

Game da hakan, Han Xu wadda daya ce daga ‘yan wasan kwallon kwando ta kasar Sin, ta ce wasan “Gu-Ma” na bayyana kyawu da kwarin gwiwar mata.

A nata bangare kuwa, jami’a a gundumar Leishan Li Xue, cewa ta yi masu halartar gasar sun fito ne daga sama da rukunonin kabilu 10, kuma "Gu-Ma" ya bunkasa musaya, da dunkulewa tsakanin kabilu daban daban.

A cewar ta "A filin wasa suna fafatawa da juna, amma da zarar sun fito sun zama abokai, suna halartar liyafa tare bayan kammala wasa".