Amurka na dauke da nauyin dakatar da kisan fararen hula a Rafah
2024-03-21 16:51:45 CMG Hausa
Yayin da dubban Falasdinawa dake arewacin zirin Gaza ke tserewa zuwa kudanci, sakamakon yakin da sojojin Isra’ila suka kaddamar na murkushe kungiyar Hamas tun daga ranar 7 ga watan Oktoban bara, masharhanta da dama na ganin lokaci na kara kurewa, na kawo karshen wannan tashin hankali, duba da cewa ga alama matakan sojin da Isra’ilan ke dauka ba abu ne da zai kare a nan kusa ba.
Ya zuwa yanzu, hare-haren sojojin Isra’ila sun kora sama da mutune miliyan guda wani lungu dake kudancin Gaza, inda birnin Rafah ya zamo “Gaba kura baya sayaki” ga masu tserewa hare-haren Isra’ila.
Duk da jan hankali da aka sha yi masa, firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, ya dage cewa sai sojojinsa sun kaddamar da hare-hare a Rafah. Alkaluma sun nuna cewa, kafin wannan tashin hankali, Rafah na da kimanin mutane 275,000 ne kacal, amma yanzu mutane sama da miliyan 1.4 ke cunkushe a cikinsa, a yanayi na matukar bukatar jin kai.
Majalissar Dinkin Duniya, da kungiyar tarayyar Turai ta EU, sun nuna damuwa game da mummunan tasirin da hare-hare a Rafah za su yi ga fararen hula. A daya hannun kuma, a baya bayan nan ita ma kasar Sin ta bayyana damuwa, game da yadda rikicin Falasdinu da Isra’ila ya haura watanni 5, kana yanayin jin kai a wurin ke kara tabarbarewa, don haka ta bayyana wajibcin gaggauta tsagaita wuta nan take, da yin iyakacin kokarin kiyaye rayukan fararen hula, da kuma rage matsalolin jin kai.
Mun san dai da fari, Amurka na sahun gaba wajen marawa Isra’ila baya a wannan yaki mai muni, amma a yanzu ta fara sauya matsaya, har ma an jiyo shugaba Joe Biden na Amurkan na cewa, kaiwa birnin Rafah hare-hare zai zama kuskure mai matukar muni.
La’akari da goyon baya da Amurkan ta nunawa Isra’ila tsawon lokaci kan wannan batu, ta hanyar maimaita dakatar da kudurin kwamitin tsaron MDD game da tsagaita wuta a Gaza, da tarin makamai da ta rika aikewa Isra’ila, da ma yadda kalaman sauya matsayar ta suka fara sanya Isra’ilan nuna alamun sassautawa. Muna iya cewa idan akwai wani karfi da zai iya sauya yanayin da ake ciki a Gaza ba zai wuce Amurka ba. Ko da yake wasu masu sharhi sun ce gwamnatin Amurka mai ci ta fara sauya matsaya ne saboda al’ummunta sun fara bore, inda a baya bayan nan masu zanga-zanga a jihar Michigan, suka rika daga kyallaye masu dauke da sakon "Idan ba a dakatar da wuta ba, ba za a yi zabe ba".
Koma dai mene ne ke faruwa a siyasar cikin gidan Amurka? Abun da ya fi damun al’ummun duniya masu son zaman lafiya, shi ne fatan ganin Amurka ta yi abun da ya dace, ta saurari ra’ayoyin sauran sassa, ta kuma goyi bayan dakatar da bude wuta a Gaza, da wanzar da zaman lafiya mai dorewa a yankin gabas ta tsakiya baki daya.(Saminu Alhassan)