logo

HAUSA

Kasar Sin Ta Jaddada Bukatar Hadin Gwiwa A Kwamitin Kare Hakkin Dan Adam Na MDD

2024-03-21 21:52:00 CMG Hausa

A ranar 20 ga wata, Chen Xu, jakadan kasar Sin a ofishin MDD dake birnin Geneva da sauran hukumomin kasa da kasa dake kasar Switzerland, ya yi jawabi a taron karo na 55 na kwamitin kare hakkin dan Adam karkashin MDD, a madadin kungiyar abokai masu neman raya harkar kare hakkin dan Adam ta hanyar musayar ra’ayi da hadin kai, inda jami’in na kasar Sin ya jaddada cewa, ya kamata a inganta aikin kare hakkin dan Adam ta hanyar musayar ra’ayi da kokarin hadin gwiwa, kuma kar a mai da hakkin dan Adam wani batu na siyasa, ko kuma fakewa da shi don neman biyan bukatar kai. (Bello Wang)