Shugaban OPEC ya jaddada hadin gwiwar makamashi da kasar Sin
2024-03-21 14:04:51 CMG Hausa
Babban sakatare na kungiyar kasashe masu arzikin man fetur (OPEC) Haitham Al Ghais, ya bayyana muhimmancin dangantakar da ke tsakanin kungiyar da kasar Sin a fannin makamashi, ya kuma yi kira da a kara inganta hadin gwiwar makamashi tare da kasa mafi karfin tattalin arziki na biyu a duniya.
Kungiyar ta OPEC da kasashe mambobinta za su ci gaba da samar da makamashi da kasar Sin ke bukata don biyan bukatunta na makamashi da ke karuwa, yayin da hadin gwiwarmu a fannin makamashi zai yi nuni da karfin dangantakarmu, a cewar Al Ghais a taron kolin kungiyar ta OPEC da Sin karo na 7 a birnin Vienna a ranar Talata.
Taron ya tattaro masana don yin musayar ra'ayi kan hasashen kasuwa da canjin makamashi. A cikin wata sanarwa da kungiyar ta OPEC ta fitar ta ce, sun yaba da ci gaban da ake samu a hadin gwiwa tsakanin kungiyar OPEC da kasar Sin bisa tsarin dandalin tattaunawa kan makamashi na OPEC da kasar Sin, tare da bayyana kudurinsu na inganta hadin gwiwar dake tsakanin bangarorin biyu, ciki har a matakan fasaha da na bincike. (Yahaya)