logo

HAUSA

Sin ta yi kira ga bangarori masu alaka da rikicin Sudan da su dakatar da bude wuta a Ramadan

2024-03-21 11:36:25 CGTN HAUSA

 

Jiya Laraba, mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin dake MDD Dai Bing ya yi kira ga bangarorin biyu masu alaka da rikicin Sudan da su aiwatar da kuduri mai lamba 2724 na kwamitin majalisar, su gaggauta tsagaita bude wuta a Ramadan, don kokarin kawar da asarar fararen hula da hana rikicin bazuwa cikin kasashen dake dab da ita.

Dai Bing ya bayyana a gun taron tattaunawa kan matsalar hatsi a Sudan cewa, an dade ana fama da rikici a Sudan, har matsalar jin kai na kara tsananta, fararen hula fiye da miliyan 18 suna fama da yunwa, karancin abinci ya zama matsala mafi jawo hankali a wasu wurare. Sin ta yabawa ayyukan da hukumar jin kai ta MDD ke gudanarwa, kuma tana mai fatan mahukuntan Sudan za su bude karin tasoshin bincike dake kan iyakar kasa da kasa don jigilar kayayyakin jin kai, kana a dauki matakin da ya dace don taka rawar gani wajen taimakawa ayyukan jin kai. Ban da wannan kuma, ya yi kira ga bangarori daban-daban su ci gaba da ba da tabbaci ga shigar da tallafin jin kai cikin sauri da tsaron da babu shingaye.

Kazalika, Dai Bing ya nanata cewa, tun barkewar rikicin, Sin tana kokarin taka rawar gani wajen samarwa Sudan kayayyakin jiyya da abinci ta hanyar hadin kai da saura. Sin kuma za ta ci gaba da hadin gwiwa da kasashen duniya don ganin an kwantar da rikicin Sudan da tabbatar da zaman lafiya mai karko. (Amina Xu)