logo

HAUSA

Kakaki: Sakatare Janar MDD ya firgita matuka dangane da farmakin da Isra'ila ta kai a asibitin Al-Shifa na Gaza

2024-03-21 14:06:44 CMG Hausa

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya firgita matuka dangane da farmakin da sojojin Isra'ila suka kai a asibitin Al-Shifa na Gaza, a cewar Florencia Soto Nino mai magana da yawun Guterres a ranar Laraba.

Florencia ta ce "Muna nanata cewa dole ne dukkan bangarorin su bi dokokin jin kai na kasa da kasa, kuma asibitoci za su iya rasa matsayinsu na wurin ba da kariya idan ba a yi amfani da su don ayyukan jin kai ba."

Ofishin kula da ayyukan jin kai na MDD wato OCHA ya bayyana cewa, a ranar Laraba ne farmakin da sojojin Isra’ila ke kai wa ciki da kewayen asibitin Al-Shifa da ke birnin Gaza ya cika kwanaki uku a jere. Rundunar sojin Isra'ila ta ce, an kashe Falasdinawa kusan 90 dauke da makamai tare da tsare wasu 300 da ake zargi.

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya fada a ranar Laraba cewa, ana shirin kai farmaki a Rafah, da ke can cikin kudancin Gaza, amma kaddamar da harin "zai dauki wani lokaci."

Firaministan ya fada a cikin wata sanarwa ta faifan bidiyo cewa "nan ba da jimawa ba" zai amince da shirin kwashe fararen hula daga Rafah, inda Falasdinawa kusan miliyan 1.5 ke samun mafaka. (Yahaya)