logo

HAUSA

"Tutar Dimokuradiyya" da kasar Amurka ta rike ta lalace

2024-03-21 16:32:36 CMG Hausa

Kasar Amurka kullum tana rike da "tutar Dimokuradiyya" a hannunta, don neman ba da umarni ga sauran kasashe, ko da yake "tutar" ta riga ta lalace, har ta zama tamkar tsumma, sakamakon matakan da kasar ta dauka masu sabawa ruhin Dimokuradiyya.

Domin yi muku karin haske, zan dauki batun korar sojojin Amurka da kasar Nijar ta yi a matsayin misali. Cikin sauki ana iya fahimtar ra'ayin gwamnatin sojojin jamhuriyar Nijar, wato wa zai iya hakuri da wani "malami" mai girman kai, da ya zo gidanka musamman ma domin yi maka lakca kan tsarin Dimokuradiyya?

Ko da yake Nijar ta riga ta yi alkawarin dawo da aikin tsarin mulkin kasar cikin sauri, amma duk da haka, Amurka ta matsa mata lamba, da neman tsoma baki cikin harkokin kasar na diplomasiya, gami da ci gaba da girke sojoji a kasar don tabbatar da "komawarta kan turbar Dimokuradiyya". Shin wane ne zai iya hakuri da hakan?

Kasar Amurka ta dade tana kallon kanta a matsayin "shugabar kasashe masu Dimokuradiyya", wadda ke da ikon saka ma sauran kasashe take na "mai Dimokuradiyya" da "mai mulkin kama-karya", sa'an nan ta matsa wa "masu mulkin kama-karya" lamba da saka musu takunkumai. Ban da haka, kasar na kokarin kulla kawance na kasashe "masu Dimokuradiyya", don neman mayar da sauran kasashe saniyar ware. Wannan mataki tamkar manufar wariya a fannin harkar siyasar kasa da kasa ne.

A kan samu wasu matakan wariya a duniyarmu, sakamakon yunkurin kasar Amurka na raba kawunan kasashen duniya. Misali, a kwanan baya, kasar Amurka ta sake gudanar da "taron koli na Dimokuradiyya", wanda kasar Koriya ta Kudu ta karbi bakuncinsa a wannan karo. Ko da yake wurin da aka yi taron na kusa da kasar Sin da kasar Rasha, amma ba a gayyace su ba. Maimakon haka, an gayyaci jami'an yankin Taiwan na kasar Sin, wanda ba shi da ikon hulda da sauran kasashe a matsayin kasa. Ganin wannan matakin da aka dauka ya sa mutum fahimtar ma'anarsa ta tsokana, shi ya sa wani mai sharhi dan kasar Ghana mai suna Yirenkyi Jesse ya rubuta cikin wani sharhinsa a jaridar “Standard” ta kasar Kenya cewa "taron kolin Dimokuradiyyar a hakika bai nuna ra'ayin Dimokuradiyya ba ko kadan. Ban da haka an ga ya nuna girman kai na kasar Amurka, da manufarta ta raba kafa dangane da batun dimokuradiyya. "

Sai dai matakan kasar Amurka su kan sa mutanen duniya mamaki, da son sanin dalilin da ya sa kasar ke kallon kanta a matsayin mai ikon nuna yatsa ga sauran kasashe.

Mene ne yanayin da ake ciki a fannin tsarin Dimokuradiyya, cikin gidan kasar Amurka? Bisa binciken ra'ayin jama'a da kafar watsa labarai ta kasar Sin CGTN, da jami'ar Renmin ta kasar suka gudanar a kwanan baya, kan wasu mutane 39315 daga kasashe 32, kashi 71.1% na mutanen na ganin cewa, akwai dimbin kuskure cikin tsarin siyasar kasar Amurka, wadanda suka sabawa ruhin Dimokuradiyya, kana tsarin Dimokuradiyya mai salon Amurka ya haddasa wa kasar matsaloli irinsu: Masu hannu da shuni na mallakar ikon mulki, da rashin dabarar daidaita harkokin zaman al'umma, da samun rarrabuwar kawunan jama'ar kasar, da rashin imani kan gwamnati, da dai sauransu.

Kana sakamakon binciken ra'ayin jama’a da kafofin watsa labaru na kasar Amurka suka gudanar a kasarsu, shi ma ya nuna ra'ayi kusan iri daya ne, inda kimanin kashi 2 bisa 3 na jama'ar kasar Amurka da aka yi musu tambaya, suka ce gwamnatin kasar ta kasa wakiltar ra'ayoyin jama'ar kasar, a dimbin matakan da ta dauka masu alaka da tattalin arziki, da bakin haure, da shawo kan bindigogi, da dai sauransu.

Sa'an nan a fannin harkar kasa da kasa, ko da yake kasar Amurka ta lakabawa kanta "mai kare Dimokuradiyya a duniya", amma hakika ba ta taba amincewa da matakan Dimokuradiyya ta fuskar al'amuran kasa da kasa ba. Maimakon haka ta rungumi manufar "kashin dankali", daidai kamar yadda sakataren harkokin wajen kasar Antony Blinken ya fada a taron tsaro na Munich da ya gudana a kwanan baya, inda ya ce "Ta fuskar al'amuran kasa da kasa, idan ba ka zama mai cin abinci ba, to, mai yiwuwa ka zama abincin da za a ci. " Wannan manufar ta haifar da dimbin wahalhalu ga sauran kasashe, duk lokacin da Amurka ke neman "kare Dimokuradiyya" a duniya. Za a iya tambayar mutanen kasashen Iraki, da Libya, da Afghanistan, da Sham, ko sun yarda da matakan kasar Amurka na yayata tsarin Dimokuradiyya a kasashensu? Ai kun san ba zai yiwu ba.

Hakika Dimokuradiyya wani abu ne da dukkan mutanen duniya ke daukakawa da darajanta. Akasarin kasashen duniya suna kokarin raya Dimokuradiyya, da neman tabbatar da shi a gidajensu. Saboda haka, kowanensu na da wani tsari na kansa, maimakon a ce akwai wani daidaitaccen tsarin Dimokuradiyya daya tak a duniya.

Dangane da ruhin Dimokuradiyya, na ga yadda masana na kasashe daban daban suka rubuta bayanai kusan iri daya, wadanda suka shafi kasancewar tsare-tsaren Dimokuradiyya daban daban, da girmama mabambantan ra'ayoyi, da kokarin samar da alfanu ga dan Adam, da dai sauransu. Don haka bisa kalamansu, za mu iya gane cewa, "tutar Dimokuradiyya" da kasar Amurka ta rike ta riga ta lalace sosai, har ma ba za iya gane yanayin ta ba. (Bello Wang)