logo

HAUSA

Ko dimokuradiyya irin ta Amurka za ta iya ceton kasashen duniya gaba daya?

2024-03-20 09:11:29 CMG Hausa

Kusan shekaru talatin ke nan bayan da aka kawo karshen yakin cacar baka, kuma ake ta kokarin tabbatar tsarin shugabancin da ya fi dacewa ga kasashen duniya. Dimokuradiyya dai ta kasance tsarin gwamnati wanda zai iya samar da tsaro mai dorewa da wadata, da cikakken ’yanci ga dukkan bil’adama. Amma tambayar ita ce, shin wace irin dimokuradiyya ce ta fi dacewa ga kasashen duniya la’akari da bambance-bambancen al’adu da tsarin zamantakewa da wayewar kai? Mun ga yadda shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya karfafa iko ta hanyar yin aiki tukuru da biyan bukatun jama’ar kasar Sin bisa wani ma’aunin da ba a taba ganin irinsa ba tun bayan shugaba Mao, da kuma yadda kasar Sin take taka rawar gani a fannin tafiyar da harkokin duniya ba tare da katsalandan a harkokin cikin gidan sauran kasashe ba. Muna ganin irin tasirin da shugabancin Hadaddiyar Daular Larabawa da wasu kasashen labarawa ke yi ga al’ummunsu, da sauran shugabannin kasashe da suka yi nasarar tafiyar da mulkin kasashensu cikin kwanciyar hankali da lumana. Amma kasar Amurka ta nace sai duniya ta bi tsarin dimokuradiyyarta kafin a zauna lafiya, tambayar it ace, Ko dimokuradiyya irin ta Amurka za ta iya ceton kasashen duniya gaba daya?  

Binciken masana ya nuna cewa, Amurka ta tafka manyan kurakurai guda hudu wajen yayata manufar dimokuradiyya a kasashen waje. Yayin da masu tsara manufofin Amurka suka mayar da hankali kan dokoki da wasu cibiyoyi a wasu kasashe don tabbatar da tsarin dimokuradiyya sai suka yi watsi al'adu, da tsarin zamantakewa, da irin wayewar kai wadanda ke tasiri ga siyasa da ci gaban wadannan kasashe. Suke tsoma baki cikin harkokin kasashen da amfani da karfin soja don tallata dabi'un dimokuradiyya ba tare da yin la'akari da matsalolin da suke haifarwa ba, tare da yin watsi da dabi'u da bukatun wadanda suke fatan shawo kan su.

A cikin shekaru arba'in da suka gabata, mun ga yadda wasu kasashen duniya suka zabi salon dimokuradiyya daidai da tarihinsu da bukatunsu, har zuwa kwanan nan tsarin dimokuradiyya mai sassaucin ra'ayi, ya mamaye Sweden, Norway, Belgium da Ireland wadda ke daidai da tattalin arzikinsu. Ga kasar Sin wadda a da take a matsayi daya da Najeriya a girman tattalin arziki yanzu ita ce a matsayi na biyu mafi girma a cikin tattalin arziki a duniya.    

Lallai a bar ko wace kasa ta zabi tsarin mulkinta daidai da tarihi, bukatu, al’adu da irin wayewar kan al’ummarta, wannan ita ce hanyar da za ta tabbatar da zaman lafiya a duniya baki daya. (Sanusi Chen, Mohammed Yahaya, Saminu Alhassan)