logo

HAUSA

Manzon musamman na shugaban kasar Sin zai halarci taron koli kan makamashin nukiliya

2024-03-20 11:43:44 CGTN HAUSA

 

Mai magana da yawun hukumar makamashin nukiliya ta kasar Sin ya bayyana a jiya Talata cewa, bisa gayyatar da aka masa, manzon musamman na Xi Jinping, shugaban kasar Sin, kana mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin JKS, kuma mataimakin firaministan kasar Sin Zhang Guoqing, zai halarci taron koli kan makamashin nukiliya na kasa da kasa karo na farko da za a gudana a Belgium daga ran 20 zuwa 22 ga watan nan da muke ciki. (Amina Xu)