logo

HAUSA

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta baiwa masu zuba jari ’yan kasashen waje damar fitar da ribar da suka samu

2024-03-20 09:20:02 CMG Hausa

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bawai dukkan ’yan kasuwa na kasashen waje da suka zuba jarinsu a kasar damar fitar da ribarsu daga kasar a duk lokacin da suke bukata ba tare da fargabar za a hana su ba.

Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasar Alhaji Muhammad Idris ne ya tabbatar da hakan a birnin Abuja lokacin da ya karbi bakuncin kungiyar raya tattalin arzikin shiyyar arewacin kasar, inda ya ce dukkan manufofin gwamnatin Najeriya kan harkokin zuba jari ba su da tsauri.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Ministan yada labaran na tarayyar Najeriya ya ce, ko da sanya hannu kan dokar sha’anin albarkatun mai da shugaban kasa ya yi a kwanan nan, ya kara haskawa masu saka jari cewa gwamnatin tarayyar Najeriya a shirye take ta samar da yanayi mai kyaun gaske a kasuwar hada-hada ta kasa da kasa a bangaren mai da sauran bangarorin da ba su da nasaba da man fetur.

Ya ci gaba da cewa, gyare-gyaren manufofin tattalin arziki da ake yi a halin yanzu a kasar ya fara haifar da sakamakon ingantacce ga wadatuwar al’amura ci gaba a kasa, domin kuwa kamar yadda mizanin tattalin arziki ya nuna Najeriya za ta fara amfana sosai da dimbin albarkatun da ake da su, haka zalika su ma masu zuba jarin za su rinka cin gajiya sosai daga jarin da suka zuba.

“Kowanne dan kasuwa da ya shigo da kudinsa cikin kasar nan domin zuba jari, gwamnati ta ba shi damar dauke ribar da ya samu a duk lokacin da ya bukata idan har dai ya bi ka’idoji da sharuddan da aka gindaya.”

A jawabinsa shugaban kungiyar Alhaji Ibrahim Yahaya ya bayyana cewa, Najeriya tana dimbin albarkatun kasa da ya kamata gwamnati ta alkinta baya ga man fetur, a don haka nema ya bukaci gwamnatin tarayayr da ta sake lalubo irin wadanann dimbin albarkatu wanda akwai su da yawa a shiyyar arewacin kasar. (Garba Abdullahi Bagwai)