logo

HAUSA

Yunkurin yin katsa landan ba zai dakile ci gaban yankin HK ba

2024-03-20 20:55:01 CMG Hausa

Kamar dai yadda aka yi tsammani, bayan majalissar dokokin HK ta zartas da kudurin dokar tsaron kasa da gagarumin rinjaye a baya bayan nan, ta kuma cimma nasarar kammala sashe na 23, na dokar gudanarwar yankin na musamman na Sin a ranar 19 ga watan nan, wasu sassa daga kasashen yamma sun zabura, wajen fara sukar wannan mataki, suna masu cewa hanya ce ta dakushe ‘yancin bil adama, kana wasu sun rika nuna shakku, game da yanayin da yankin na HK zai shiga ta fuskar hada hadar kasuwanci.

Amma abun tambaya a nan shi ne, shin wajibi ne a samar da wannan doka ta tsaro? Kuma mene ne ma’anarta ga yankin HK? Alal hakika, zarge-zarge, da kazafi da wadancan sassa suka yiwa Sin ba su da tushe ko makama. Kawai dai akwai wasu mutane a kasashen yamma, dake gudanar da wasan kwaikwayon siyasa da suka saba.

Ya zuwa yau, mutane sun kara fahimtar wajibcin wannan doka ta tsaron kasa, la’akari da yamutsin da yankin HK ya sha fama da shi mai nasaba da yunkurin “samun ‘yancin kai”, da tashin hankalin da ya biyo bayan hakan, yayin gyaran dokokin jagorancin yankin.

A shekarar 2020 ne aka tsara dokar tsaron kasa ta yankin HK, aka kuma aiwatar da ita, wadda ta zama ginshikin samun wadata da daidaito a yankin. Yanzu haka shekaru 3 sun shude bayan wannan ci gaba, kuma tuni yankin HK ya sauya daga wurin da ya sha fama da tashe tashen hankula, zuwa wuri mai cikakken tsarin jagoranci da walwala. To sai dai kuma a daya hannun, kalubalen tsaron kasa da yankin ke fuskanta har yanzu yana da sarkakiya da tsanani.

Wannan doka ta tsaron kasa ta HK, da sauran dokokin da ake aiwatarwa a yankin na musamman na Sin, ba su kai ga wadatarwa wajen shawo kan dukkanin dabi’u, da ayyuka dake iya haifar da barazana ga tsaron kasa ba. Zartas da wannan doka ta yankin HK a wannan karo, na da nasaba da aiwatar da kudurorin tsaron kasa na HK, da cike gibin manufar tabbatar da tsaro a HK, da tabbatar da wanzuwar daidaito na dogon lokaci a HK, da ma cimma nasarar gudanar da manufar nan ta “kasa daya tsarin mulki biyu” bisa daidaito.  (Saminu Alhassan)