logo

HAUSA

Majalisar dattawan Najeriya ta kaddamar da bincike kan kashe sojoji a yankin Delta

2024-03-20 12:10:50 CMG Hausa

Majalisar dattawan Najeriya ta kaddamar da bincike a ranar Talata kan kisan da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka yi wa wasu sojojin da ke aikin samar da zaman lafiya a wani kauyen da ke yankin Delta a kwanan nan.

A kalla jami’an sojin Najeriya 16 da suka hada da kwamanda daya, da wasu manjo biyu da kyaftin daya da sojoji 12 ne aka kashe a harin da aka kai a ranar Alhamis da ta gabata a yankin Okuama da ke karamar hukumar Ughelli ta kudu a jihar Delta mai arzikin man fetur, kamar yadda majalisar dattawan ta bayyana a zamanta na ranar Talata.

Majalisar dattawan ta umurci kwamitinta kan tsaro da ya yi bincike sosai kan lamarin. Kazalika, majalisar dattawan Najeriya ta yi kira ga gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro da su gaggauta gano tare da kama wadanda suka aikata wannan danyen aiki, inda suka bukaci da a gurfanar da su gaban kuliya su fuskanci sakamakon abin da suka aikata ta hanyar adalci da tsarin shari'a na gaskiya. (Yahaya)