logo

HAUSA

Wang Yi ya yi tsokaci kan basirar bunkasuwar huldar Sin da Austriliya

2024-03-20 11:52:41 CGTN HAUSA

 

Ran 20 ga wata agogon Canberra, babban birnin Austriliya, mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, kana ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya yi shawarwari kan diplomasiyya da manyan tsare-tsare karo na 7 da takwararsa Penny Wong ta kasar Austriliya.

Wang Yi ya ce, ziyararsa a wannan karo ya yi daidai lokacin cika shekaru 10 da ziyarar aikin shugaba Xi Jinping na kasar Sin a kasar Austriliya da ma kafa huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin kasashen biyu a dukkan fannoni. Wannan shekara ta kasance mahada ce na da da nan gaba. Kamata ya yi bangarorin biyu su gaggauta hadin gwiwarsu bisa tushe mai kyau, da daukar matakai masu yakini ta yadda za su inganta huldarsu mai armashi.

A cewarsa, huldar bangarorin biyu a cikin shekaru 10 da suka gabata, ta gabatar da abubuwan koyi da kuma basira da dabaru. Abin da aka sa gaba shi ne, mutunta juna. Sin ba ta tsoma baki cikin harkokin gidan kasar Austriliya ba, kuma ta mutunta tsari da hanyar da kasar Austriliya ta zaba. Don haka, ya yi fatan, gwamantin Austriliya ta cika alkawarin da ta yi tun kafuwar huldarsu, game da ikon mulki da mutunci da muradun kasar Sin, da kuma daidaita harkokin dake da nasaba da kasar Sin cikin tsanaki. (Amina Xu)