logo

HAUSA

Yankin masana’antun Habasha da Sin ta gina ya samar da dalar Amurka miliyan 20 daga kayayyakin da ake fitarwa a cikin watannin 6

2024-03-20 12:08:52 CMG Hausa


Kamfanin dillancin labarai na kasar Habasha ya bayar da rahoton cewa, gwamnatin kasar Habasha ta samu kudaden shiga na kusan dalar Amurka 20 a cikin watannin shida daga kayayyakin da take fitarwa zuwa kasashen waje da take samarwa a yankin masana’antun kasar na Hassawa da kasar Sin ta gina.

Ana sa ran yankin na Hassawa zai samar da kusan dalar Amurka miliyan 44 daga fitar da kayayyakin da masana’antun ke samarwa a cikin shekarar kasafin kudin Habasha ta 2023 zuwa 2024, wanda ya fara a ranar 8 ga watan Yuli, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasar Habasha (ENA) ya nakalto daga Mathiwos Ashenafi, babban manajan yankin.

An gina yankin masana’antun a birnin Hawassa da ke kudancin kasar Habasha, mai nisan kilomita 275 kudu da Addis Ababa babban birnin kasar, ana daukarsa a matsayin babban wurin da masana'antun ketare ke amfani da shi a kasar ta gabashin Afirka, wajen aikin samar da yadi, tufafi da kayayyakin kwalliyar tufafi. (Yahaya)