logo

HAUSA

Tallafin da Amurka ta baiwa Gaza wasan kwaikwayo ne

2024-03-20 12:22:08 CGTN HAUSA

Kwanan baya, Isra’ila ta kara kaiwa zirin Gaza hare-hare, lamarin da ya yi sanadin asarar rayuwa da dama. Amurka ce ta tallafi wasu daga cikin makaman da Isra’ila ta yi amfani da su. Bisa labarin da shafin yanar gizo na jaridar kasan Isra’ila wato Ha'aretz ya bayar, an cewa, daga sansanonin soja da makaman da Amurka ta jibge a sassan duniya, a cikin watanni 5 da suka gabata, Amurka ta yi jigilar makamai zuwa Isra’ila na adadin da ba a taba gani ba.

Abun mamaki shi ne, a wani bangare Amurka na tallafawa Isra’ila da makamai, yayin da a wani bangare na daban kuwa, ta yanke shawarar jefawa fararen hula a Gaza abinci daga sama. Abinci fiye da dubu da Amurka ta jefa daga sama, yawancinsu na fadawa ne cikin teku, ta yadda ba za su biya bukatun fararen hular Gaza da yawansu ya haura miliyan 2 ba. Ban da wannan kuma, mutane 5 sun mutu, saboda laimar sauka daga jirgin sama masu dauke da abincin sun gaza budewa cikin lokaci, hakan ya sa abincin ya fada kai tsaye kan wasu gidaje dake kasa. Shin ko Amurka tana mai da hankali kan rikicin jin kai dake barkewa a Gaza?

Kungiyoyin jin kai da dama sun yi tir da hanyar da Amurka ta zaba ta samar da tallafin jin kai ta hanyar jefa abinci daga sama. A ganinsu, matakin da ya fi kyau shi ne Amurka ta kalubalanci kawarta wato Isra’ila da ta bude hanyoyin jin kai, ko daina samarwa Isra’ila makamai. Ainihin muradun ‘yan siyasar Amurka shi ne, yunkuri samun goyon baya daga masu kada kuri’u a gida.

Ban da wannan kuma, shugaban kasar Joseph Biden ya sanar da shirin kafa wata tashar jirgin ruwa ta wucin gadi a gabar tekun bahar rum dake Gaza, don baiwa yankin tallafin jin kai. Wasu abokai kan yanar gizo sun yi zargin cewa, Amurka tana da karfin dakatar da rikicin da ake fuskanta a Gaza muddin ta daina samarwa Isra’ila makamai, amma ta yi wasan kwaikwayo na samar da tallafin jin kai.

Tallafin da Amurka ta bayar da kyar sun isa hannun fararen hula, amma makaman da ta samar ta kwace rayuka masu dimbin yawa. ‘Yan siyasar Amurka su kan yi wasan kwaikwayo don samun kuri’u, amma a wannan karo masu gudun hijira ke yin asara, wadanda ba su da abinci basu da gidaje kuma ba su da tsaro, ballantana hakkin Bil Adama. Shin ko ‘yan siyasar Amurka ba su jin kunya? (Mai zana da rubutu: MINA)