logo

HAUSA

Kasar Sin ta yi kira ga kasa da kasa su hada hannu wajen rage yawan makaman nukiliya

2024-03-19 16:12:26 CMG Hausa

Zaunannen wakilin Sin a MDD Zhang Jun, ya ce ksar Sin za ta hada hannu da kasa da kasa wajen rage yawan makaman nukiliya da kwance damararsu.

Zhang Jun ya shaidawa Kwamitin Sulhu na majalisar cewa, har kullum kasar Sin na goyon bayan haramtawa da lalata makaman nukiliya baki daya. Kuma ba tare da la’akari da irin sauyin da duniya za ta gani ba, kasar Sin za ta girmama kudurinta na kaucewa fara amfani da makaman nukiliya kan wata kasa, kuma za ta nace ga amfani da nukiliya ne a matsayin dabarar kare kai, sannan ba za ta shiga duk wani nau’in gasar tara makaman nukiliyar ba.

Ya kara da cewa, kasar za ta ci gaba da nacewa wajen ganin nukiliyarta na wani mataki mafi karanci da ake bukata na tsaron kai, da ci gaba da hada hannu da kasa da kasa wajen kwance damarar makaman da rage yawansu. (Fa’iza Mustapha)