logo

HAUSA

Sani Abdulkarim: Akwai damammaki da yawa a kasar Sin!

2024-03-19 15:34:22 CMG Hausa

Sani Abdulkarim, dan asalin jihar Kanon Najeriya ne, kuma malami daga jami’ar kimiyya da fasaha ta Wudil dake jihar Kano, wanda a yanzu haka yake karatun digiri na uku a wata jami’a dake nan birnin Beijing na kasar Sin, mai suna University of Science and Technology Beijing.

A zantawarsa da Murtala Zhang, malam Sani ya bayyana ra’ayinsa kan ci gaban kasar Sin, da abubuwan da ya jawo hankalinsa a kasar, gami da bambancin yanayin karatu tsakanin gida Najeriya da Sin.

A karshe, malam Sani ya ce, akwai damammaki da yawa a kasar Sin, musamman a fannonin ilimin zamani da kasuwanci, don haka yana kira ga mutanen Najeriya, musamman matasa, da su tashi tsaye don kulla alaka da kasar Sin. (Murtala Zhang)