logo

HAUSA

Abdourahamne Tiani ya aika sakon taya murna ga Vladmir Putin bisa ga sake lashe zaben shugaban kasar Rasha

2024-03-19 10:43:33 CMG Hausa

A jamhuriyyar Nijar, shugaban kasar Abdrouhamane Tiani, ya aika da sakon taya murna a ranar jiya Litinin 18 ga watan Maris din shekarar 2024 zuwa ga shugaban kasar Rasha Vladmir Putin, da ya sake lashe zaben shugaban kasa.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto. 

Bayan zaben shugaban kasar Rasha da aka gudanar a makon da ya gabata tare da nasarar shugaba mai ci na Rasha Vladmir Putin da kashi 87. 97 cikin 100 na kuri’un da ’yan kasar suka jefa, bisa ga sakamakon da babbar hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar Rasha ta bakin shugabarta madam Ella Pamfilova ta tabbatar ta gidan talabijin din kasar a ranar Lahadi 17 ga watan Maris din shekarar 2024 bisa ga nasarar shugaba Vladmir Putin.

Kamar sauran shugabannin kasashen duniya, shugaban kasar Nijar ma Abdrouhamane Tiani, ya aika sakon taya murna ga takwaransa na kasar Rasha Vladmir Putin. Sakon na cewa, “bisa ga wannan nasara ce, a matsayina na shugaban kwamitin ceton kasa na CNSP nike isar da jinjina ta musamman da taya murna ga shugaban kasar Rasha, Vladmir Puti bisa ga wannan nasara.”

Sakon kuma, ya ci gaba da cewa, kasar Nijar, domin neman ’yancin kanta da na al’ummarta, da kuma bunkasuwarta, ba za ta kasa a gwiwa ba, na nuna alfaharinta na ganin taimakonku kan hanyar da kasar Nijar ta dauka domin ci gabanta, da yaukaka huldar dangantaka tare da kasar Rasha domin ganin Nijar ta cimma wannan nasara ta kokowar neman ’yancin kanta da kishin kasarta, in ji wannan sako a karshe.

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.