logo

HAUSA

Babban hafsan tsaron Najeriya ya isa garin Kaduna bayan samun rahoton sace karin mutane 87

2024-03-19 10:34:10 CMG Hausa

Babban hafsan tsaron Najeriya Janaral Christopher Musa ya bukaci al’ummar kasar da kada su karaya a kan karuwar sace-sacen jama’a da yanzu haka ke faruwa a wasu sassa na arewacin kasar.

Ya bukaci hakan ne lokacin da ya ziyarci gwamnan jihar Kaduna bayan sa’o’i da sake samun labarin sace karin wasu mutane 87 a wani harin da aka kai yankin Kajuru dake jihar Kaduna a daren Lahadi 17 ga wata.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Janaral Christopher Musa ya shaidawa gwamnan na jihar Kaduna cewa ya ziyarci gidan gwamnatin jihar ne bayan ya kai ziyara yankin tashar Kajuru wurin da ’yan bindiga suka kai hari har suka sace mutane 87, sannan kuma suka fasa shaguna tare da debe kayan abinci da sauran kayayyaki masu daraja.

Ya ja hankalin masu daurewa irin wadannan ’yan ta’adda gindi cewa, ba za su taba cimma burinsu ba na dakile kokarin ciyar da Najeriya gaba ta hanyar sanya fargaba a zukatan ’yan kasa da ma baki ’yan kasuwa.

Babban hafsan tsaron na Najeriya ya tabbatarwa gwamnan na jihar Kaduna cewa yanzu haka ana bakin kokari wajen ceto mutanen da aka sace a jihar wanda suka kunshi dalibai da kuma na baya bayan nan da aka sace a yankin na Kajuru.

“Muna yin wasu ’yan gyare-gyare wajen tabbatar da ganin cewa jihar Kaduna da arewa maso yamma da ma Najeriya baki daya sun kasance cikin cikakken tsaro.”

A jawabinsa gwamnan na jihar ta Kaduna Sanata Uba Sani ya bayyana gamsuwa ne bisa kokarin jami’an tsaro da suka hada da sojoji da ’yan sanda dake jihar ta Kaduna wajen tabbatar da tsaro da kuma ganin an ceto mutanen da  ’yan bindiga suka sace.

Harin na daren Lahadi ya zo daidai kwanaki biyu da sace wasu mata 15 a Dogon Noma dake yankin karamar hukumar ta Kajuru a jihar Kaduna. (Garba Abdullahi Bagwai)