logo

HAUSA

Fahimtar juna tsakanin matasan Sin da Amurka zai haskaka makomar dangantakar kasashen biyu

2024-03-19 18:09:13 CMG Hausa

Babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) da kungiyar raya mu’amala tsakanin daliban Amurka da Sin, sun kaddamar da bikin raya mu’amalar matasa da yaran Sin da Amurka mai taken “Zuwan Abokai Daga Nesa”, a jiya Litinin a nan birnin Beijing, wanda ya kasance wani bangare na mu’amala tsakanin matasan Amurka dubu 50 dake ziyara a Sin, da kuma takwarorinsu na kasar Sin.

Da farko, a matsayinta na kafar yada labarai, CMG ba ta tsaya ga bayar da labaran kadai ba, ta zo da wani sabon salon, inda ta kasance gada tsakanin Sin da sauran sassan duniya, ta hanyar wayar da kan jama’a game da kasar Sin da kuma yayata kyawawan manufofi da dabi’u da al’adun kasar, domin su isa ga al’ummun duniya, har su kara fahimtar kasar Sin, sabanin labaran da suka saba ji daga kafafen yada labarai na yammacin duniya. 

Hakika, yadda ake samun tankiya da kalamai na rashin fahimta daga ’yan siyasar Amurka, na matukar bukatar karin fahimta da wayewar kai domin hakan ba hanya ce mai bullewa ga dangantaka tsakanin manyan kasashen ba.

Shirya tarukan inganta mu’amala da cudanya tsakanin yara da matasa irin wannan, zai bayar da  gagarumar gudunmawa wajen kyautata fahimta da alaka tsakanin zuri’o’i masu tasowa na Sin da Amurka. Kamar yadda bahaushe kan ce, “yara manyan gobe”, idan aka fara samun kyakkyawar fahimta da mu’amala tsakanin matasa da yara tun daga yanzu, to a nan gaba bangarorin biyu za su kasance aminai kuma ’yan uwa, wadanda suka san juna, suka kuma san bambance-bambacen dake akwai tsakanin al’adu da dabi’unsu, kuma suka lalubo yadda za a yi zaman jituwa da girmama juna a tsakaninsu. 

A baya bayan nan, an ga yadda dalibai da malamai na makarantar sakandare ta Lincoln ta Amurka suka aikowa shugaba Xi Jinping da Uwargidansa katin gaisuwar sabuwar shekara, inda shugaban da uwargidansa suka mayar musu da amsa, har ma da gayyatarsu zuwa kasar Sin. 

Gani ya kori ji. Gayyatar karin matasan Amurka zuwa kasar Sin, ya nuna cewa, kofar Sin a bude take, tana maraba da baki, haka kuma ba ta da wani abun boyewa. Ya kuma kara nuna kaifin basirar Sin na hangen nesa da sanin ya kamata, a kokarinta na raya dangantakarta da Amurka ta yadda makomarta za ta kasance mai haske. (Fa’iza Mustapha)