logo

HAUSA

CMG ya shirya taron tattaunawa tsakanin kafofin watsa labaran kasa da kasa a Najeriya

2024-03-19 21:10:54 CMG Hausa

A jiya Litinin 18 ga wata ne babban rukunin gidajen rediyo da talibijin na kasar Sin ko CMG a takaice, da jami’ar Abuja ta Najeriya, suka shirya taron tattaunawa tsakanin kafofin watsa labarai na kasa da kasa mai taken “Kasar Sin a yanayin bazara” a birnin Abuja, fadar mulkin kasar, taron da ya samu halartar manyan baki kusan 50 daga bangarorin siyasa, da ilimi, da kafofin watsa labarai na Najeriya.

Mahalartan taron sun yi musayar ra’ayoyi tsakaninsu, kan batutuwan da suka shafi “Sabon karfin samar da hajoji, da hidimomi masu karko” da “Ci gaba mai inganci”, kuma sun tattauna kan yadda za a yi amfani da damammakin samun ci gaba na kasar Sin, da kuma yadda za a kara zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka. (Jamila)