logo

HAUSA

Kasuwar Sin Na Taimaka Dunkule Tattalin Arzikin Duniya

2024-03-18 16:13:30 CMG Hausa

A kwanan baya ne asusun ba da lamuni na duniya IMF ya sake yin kwaskwarima ga hasashen bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin a shekarar 2024, lamarin dake nuni da cewa tattalin arzikin kasar Sin na iya zarce hasashen da aka yi a baya, duba ga irin gudummawar da ta bayar wajen bunkasar tattalin arzikin duniya a shekarar 2023, wanda ya haura kashi 30 cikin 100, lamarin da ya kara tabbatar da matsayinta ta babbar kasuwa dake bunkasa tattalin arzikin duniya. Wannan kyakkyawar hangen nesa ba wai kawai yana da fa'ida ga kasar Sin ba, har ma zai yi tasiri ga ci gaban tattalin arzikin duniya baki daya, musamman ma kasashe masu tasowa.

Kasar Sin tana taka muhimmiyar rawa a fannin masana'antu da samar da kayayyaki a duniya. Ta zama cibiyar masana'antu ta duniya, yayin da take jawo hannun jari kai tsaye daga ketare tare da yin amfani da wadatar kwadago mai rahusa da inganci, da inganta ababen more rayuwa, da kwararrun ma'aikata. Kazalika, kwararrun masana'antu na musamman na kasar Sin da ingantattun tsarin samar da kayayyaki sun sa ta zama muhimmin bangare a yawancin masana'antun duniya.

Kamfanonin kasar Sin na amfani da sabbin dabarun aiki da hidimomi, tare da habaka karfinsu na sarrafa hajoji da hidimomi, da takara mai tsafta, suna zuba jari a kasuwannin kasashen waje. Kuma suna da fa'ida sosai a fannonin da suka hada da fasahohin zamani, da samar da hajoji mara gurbata muhalli, da kuma sauya akalar hada-hadar kasuwanci zuwa dijital. Sun cimma wannan nasarar ne ta hanyar zuba jari a ayyukan kirkire-kirkire a fannonin da suka hada da fasahar 5G, da kirkirarriyar basira (AI), da makamashin da ake sabuntawa, da kuma motocin lantarki wadanda suka jawo hankalin duniya.

A matsayinta na kasar da ta fi fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje, kasar Sin ta kulla huldar kasuwanci mai yawa da kasashen duniya. Alal misali, ayyukanta a karkashin shirin shawarar “ziri daya da hanya daya” (BRI) suna habaka hadin gwiwa da karfafa dangantakar tattalin arziki  da kasashe abokan huldarta. Wannan matsayi bisa manyan tsare-tsare ya baiwa kasar Sin damar taka muhimmiyar rawa wajen tsara yanayin cinikayyar duniya da inganta hadin gwiwar tattalin arziki.

Rawar gani da kasar Sin ke takawa a kasuwar duniya ya taimaka dunkule tattalin arzikin duniya. Duniya na tasirantuwa da ci gabanta kamar yadda take ba da kuzari da kwanciyar hankali ga tattalin arzikin duniya, yayin da take more damar samun ci gaba tare da sauran kasashen duniya. (Mohammed Yahaya)