Nuryan Maimaiti: jerin kogunan Kezil sun samar da damar sa kaimi ga cudanya tsakanin kabilu daban daban na jihar Xinjiang
2024-03-18 13:55:00 CMG Hausa
A makon da ya wuce, mun gabatar muku wata mace mai suna Nuryan Maimaiti, wadda ta shafe shekaru 6 tana aikin binciken rukunin kogon Kezil, wadanda ke kasancewa kogon addinin Buddha da aka gada mafi tsufa, mafi girma, mafi dadewa, mafi yawan nau'o'in, kana mafi tasiri a Yankunan Yamma, wato wurin da ake kira da gama gari a jihar Xinjiang ta kasar Sin da tsakiyar Asiya, don gano tarihin mu'amala da cudanya tsakanin kabilu daban daban na jihar Xinjiang. A cikin shirinmu na yau, za mu ci gaba da kawo muku labari ne game da wannan baiwar Allah.
A duk lokacin da ta yi magana game da kogon Kezil, Nuryan ta kan yi magana ba tare da tsayawa ba: a lokacin da tsohuwar Kucina ta zama tashar kasuwanci da ta hada babban yankin Turai da Asiya, da ma wata muhimmiyar tasha dake kan tsohuwar hanyar siliki, a lokacin ne aka kawo addinin Buddha zuwa kasar Sin.
Akwai ruwan ma'adinai mai launin shudi a jikin bangon kogon, wanda ya fito daga makwabciyar kasar Sin Afghanistan, wanda ke tabbatar da cewa, Kucina cibiyar cinikayyar waje ce ta tsohuwar kasar Sin. Zane-zanen bango da aka zana game da yadda wasu ‘yan mata ke yin kade-kade a cikin kogo mai lamba 38, sun nuna dimbin kayan kida daga tsohuwar kasar Girka, da tsohuwar Indiya, da kuma filayen tsakiyar kasar Sin, lamarin da ke nuni da haduwar al'adun kasar Sin da na yammacin duniya da aka taba yi a wurin. Kogo mai lamba 27, kogo ne mai yawan alkukai, wanda kuma ke da salon musamman na tsakiyar kasar Sin, ta haka aka gano cewa, addinin Buddha wanda aka gabatar da shi zuwa tsakiyar kasar Sin, ya habaka kuma ya sauya halinsa, bayan ya hada da al’adun yankin, sannan ya sake komawa Kucina…
Irin wadannan mu’amalar al’adu da musayar cinikayya ne ke sa kaimi ga cudanya tsakanin kabilu daban daban, wanda ya kai ga jihar Xinjiang, inda dukkanin kabilu ke rayuwa tare da samun ci gaba yadda ya kamata a yau.
Don haka, a duk lokacin da ta yi bayani, Nuryan ba ta mantawa da gaya wa masu yawon shakatawa cewa, Xinjiang wani yanki ne na kasar Sin, kuma bai taba rabuwa da kasar ba a tarihi.
A yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ke rangadin aiki a jihar Xinjiang, ya nuna cewa, an kafa tarihin Xinjiang ta hanyar yin mu'amala, al'ummar kasar Sin al'umma ce mai yawan jama'a da hadin kai, kuma kyawawan al'adun kabilu daban daban sun hade zuwa al'adun kasar Sin.
Nuryan ta amince da haka sosai. A ganinta, amincewa da al’adun kabilu daban daban na da muhimmiyar ma’ana, ta kuma kara fahimtar nauyin da ke kanta a matsayin mai yada al'adu. A idanunta, kayan tarihi masu dadadden tarihi suna da rai, wadancan jerin kogo da ke kan tsaunin duwatsu da zane-zanen bango dake cikin kogon, tamkar wani dattijo ne wanda ya sha fama da jujjuyawar rayuwa, kuma a hankali yana ba da labarin tarihi da zamani.
Aikin ba da kariya, shi ne tushen nazarin kayan tarihi. Bayan fiye da shekaru 1,700, jerin kogon Kezil sun riga sun kasance masu rauni sosai. A lokacin rani, akwai masu yawon bude ido da yawa, iskar carbon dioxide da mutane ke fitarwa na iya haifar da yanayin zafi a kogon, kuma ba za a iya shigar da na’urar sanyaya wuri cikin koguna ba, saboda busa iska mai sanyi kai tsaye zai illata zane-zanen jikin bangwayen.
Baya ga haka kuma, jihar Xinjiang tana da bambancin yanayin zafi tsakanin dare da rana, raguwar yanayin zafi zai kasance tare da hauhawar danshi, wanda kuma ba shi da kyau ga kare zane-zanen bango. Sabili da haka, wajibi ne a yi la'akari da daidaita yanayin zafi da na danshi a cikin kogon, da samar da iska mai dacewa, da kuma rufe kofofi a kan lokaci.
Nuryan tana da hakuri da kwazo wajen yin wadannan ayyuka na karshe a kowacce rana, sau da yawa ta kan hau dutsen bayan mutane sun sauko, ta kan yi sintirin kimamin sa’o’i 2 kafin ta kammala duba dukkanin kogon.
Daga birni ta fito, kuma ta na aiki akan kari a galibin lokuta, a idanun wasu mutane da dama, irin wannan halin rayuwa yana da wuyar gaske kuma ba shi da ban sha’awa, amma Nuryan tana jin dadin hakan. Ta ce, muddin an tsara aiki da kyau, kuma aka bi shi mataki-mataki a kowace rana, ba za a sha wahala sosai ba.
A da, ta kasance tana aiki a gunduma. Bayan ta gama aiki, ta kan hadu da kawaye don kallon fina-finai da cin abinci, a yanzu ta fi samun lokaci ita kadai, wanda ke ba ta karin lokacin karatu da tunani. A cewar Nuryan, ta fi son yanayin da take ciki a yanzu.
Hasali ma, rayuwar Nuryan tana da yalwa sosai, baya ga aikin nazarin kogo, tana kuma da wani matsayi na daban, wato ita ce ta kaddamar da wata kungiyar sa kai mai suna “Mu Iyali Daya ne”. Mambobin kungiyar sun fito daga kabilu daban daban, kuma suna kasancewa iyali daya mai jituwa.
Da zarar lokacin sanyi ya zo, kungiyoyin jin kai a biranen Beijing da Shenzhen da sauran wuraren kasar Sin, suna aikewa da tufafin hunturu. Nuryan da abokan aikinta su kan ware su tare da kai su ga yara mabukata a yankin, kafin dusar kankara ta rufe tsaunuka.
Nuryan marainiya ce, amma ba ta rasa iyali ba. Iyaye daga kabilar Han sun dauke ta, kuma sun reneta tun tana karama, kana kuma tana da yan uwa daga kabilar Han guda biyu. Mahaifiyarta ta rasu ne sakamakon rashin lafiya yayin da take kan hanyar neman magani, kuma iyayenta na yanzu ne suka taimaka, suka kai mahaifiyarta gida.
Irin tarihinta na musamman, yana sanya ta sha'awar samun soyayya da kuma son ba da soyayya.
A shekarar 2013, wata yarinya 'yar kabilar Uygur mai suna Rehan Guli ta gamu da tsautsayi inda ta samu kunar da ta kai kusan kashi 70% da tafasashen ruwa. Amma, saboda iyalinta ba su da isassun kudi, ta kasa samun magani.
Bayan Nuryan ta ziyarci iyalin yarinyar, ta buga wasikar neman taimako a yanar gizo, wadda ta ja hankalin mutane masu kirki suka bayar da tallafi. Ta wannan lamari ne, Nuryan ta ga irin karfin da al'umma ke da shi, ta kuma karfafa aniyarta ta gudanar da ayyukan jin kai, don haka ta kaddamar da kungiyar sa kai ta "Mu Iyali Daya ne".
A lokacin, tana aiki ne da rana, kuma tana shirya ayyukan sa kai da daddare, ciki har da jajantawa masu bukata, da ba da gudummawa, da talla da dai sauransu, kuma tana shagaltuwa sosai. Ba da dadewa ba ta zama ma'aikaciyar yin mu’ammala ta Kucha dake kula da ayyukan sa kai a karkara a jihar Xinjiang, kuma mai tsara ayyukan ba da tallafin tufafi na jihar.
Shekaru goma sun shude a cikin kiftawar ido, har yanzu kungiyar "Mu Iyali Daya ne" tana nan tana aiki, kuma ta kasance a sahun gaba a ayyukan sa kai, akwai wadanda da suka taba tambayar Nuryan, dalilin da ya sa ake kiran kungiyar ta da "Mu Iyali Daya ne", inda ta amsa da cewa, "Dukkan kabilun jihar Xinjiang suna hada kai don neman wadata tare. Don haka asalinsu iyali daya ne!"