logo

HAUSA

Hukumar kwastam a tashar ruwan Tincan Islan ta samu nasarar kame bindigu da alburusai da kuma haramtattun kwayoyi

2024-03-18 09:26:18 CMG Hausa


Ofishin hukumar kwastam na tashar ruwan Tincan Island a Legos dake kudancin Najeriya ta samu nasarar kame bindigogi kanana da manya da tarin alburusai da kuma haramtuttun kwayoyi da hodar iblis wanda aka shigo da su cikin kasar.

A lokacin da yake yi wa manema labarai bayanin nasarorin da ofishin hukumar ya samu a tsakanin watan Janairu zuwa Maris na 2024, kwantrolan hukumar mai lura da yankin tashar ruwan Mr Dera Nnadi ya ce, baya ga nasarar kame haramtattun kayayyaki haka kuma hukuma ta samu nasarar ninka adadin kudaden shigar da take Tarawa.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Kwantrolan hukumar ta kwanstam a tashar ruwan na Tincan Island ya ce, sun sami nasarar kame makaman ne da kuma kwayoyi masu sauya tunanin dan adam bisa hadin gwiwa da jami’an hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya.

Ya ce, an shigo da wadannan kayayyaki ne a cikin kwantaina kuma a lokutan daban-daban.

“Ofishin hukumar tare da hadin gwiwa da hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa ya sami nasarar kame wasu abubuwan sha masu sauya tunanin dan Adama wanda aka shigo da su cikin kasar nan.”

A jawabinsa, kwamandan hukumar NDLEA mai lura da sashen yaki da miyagun kwayoyi Alhaji Muhammad Aminu Abubakar jaddada bukatar ci gaba da aiki tare ya yi tsakanin hukumar tasu da kuma hukumar ta Kwastam.

“Kamar yadda kuke gani a nan wasu daga cikin makaman da aka kama an shigo da su ne tare da miyagun kwayoyin.”

Alhaji Muhamamad Abubakar ya ce, wannan ya nuna akwai hadin baki sosai tsakanin masu shigo da makamai da kuma dillalan miyagun kwayoyi, kuma akwai tabbacin suna da rassa ne a sassan Najeriya da ma wasu kasashe dake yammacin Afrika. (Garba Abdullahi Bagwai)