logo

HAUSA

Sarkin Lesotho na sa ran yin hadin gwiwa a babban mataki da kasar Sin

2024-03-18 11:00:36 CMG Hausa

Sarkin Lesotho Letsie III ya bayyana cewa, a cikin shekaru 30 da suka gabata, dangantakar da ke tsakanin kasashen Lesotho da Sin ta samu kyakkyawar ci gaba kuma mai inganci, kuma yana fatan dangantakar za ta ci gaba da kara karfi da karko a cikin lokuta masu zuwa.

A bana ne aka cika shekaru 30 da dawo da huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Lesotho. Letsie III ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a wata hira da aka yi da shi a gidan sarautar da ke Maseru, babban birnin kasar, cewar a karkashin wannan dangantakar, kasarsa tana amfana sosai daga taimakon da kasar Sin ke bayarwa. 

Alal misali, kasar Sin ta taimakawa kasar Lesotho sosai a fannin raya ababen more rayuwa, yana mai cewa, tare da taimakon kasar Sin, Lesotho ta gina sabbin hanyoyi, asibitoci, da ayyuka daban-daban.

Letsie III ya yaba da shirye-shiryen da kasar Sin ta gabatar, kamar shirin tallafawa masana'antu a Afirka, da shirin kasar Sin na tallafawa zamanantar da aikin gona na Afirka, da shirin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka kan raya basira.

Letsie III ya kara da cewa, Lesotho a ko da yaushe tana bin manufar Sin daya tak, kuma za ta ci gaba da nuna goyon baya ga kasar Sin wajen kara taka rawa a fagen kasa da kasa, wanda hakan zai amfanar dukkan jama'a. (Yahaya)