logo

HAUSA

Da alama Vladimir Putin ya lashe zaben shugaban kasar Rasha bayan kidaya kaso 95.04 na kuri’un da aka kada

2024-03-18 10:37:34 CMG Hausa

Bayanai na farko-farko daga hukumar zabe ta kasar Rasha sun nuna cewa, da alama shugaban kasar mai ci Vladimir Putin ne ya lashe zaben shugaban kasa karo na 8 da aka yi a kasar, inda ya samu kaso 87.32 na kuri’un da aka kada, bayan kidaya kaso 95.04 na kuri’un, zuwa yammacin jiya Lahadi.

Bisa ka’idojin zabe na kasar, dan takarar da ya samu sama da kaso 50 na kuri’u ne ya lashe zabe.

A cewar hukumar zabe ta kasar, kaso 74.22 na masu kada kuri’a ne suka fito domin zaben.

Sakamakon nazari da wata cibiyar binciken jin ra’ayin jama’a ta kasar Rasha ta gudanar ya nuna cewa, shugaba Putin zai lashe zaben da kaso 87 na kuri’u.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne Rasha ta kaddamar da zaben shugaban kasa da ya shafe kwanaki 3. Kuma hukumar zaben za ta tabbatar da sakamako na karshe ne zuwa ranar 28 ga watan nan na Maris, kana ta sanar da shi cikin kwanaki uku da tabbatarwa. (Fa’iza Mustapha)