logo

HAUSA

Mai fashin baki: Taron Amurka kan demokraddiya nuna girman kai ne

2024-03-18 15:17:17 CMG Hausa

Yirenkyi Jesse, wani mai fashin baki dan kasar Ghana, ya ce taro kan demokradiyya da Amurka ke gudanarwa shekara-shekara, wanda take ikirarin manufarsa ita ce yayata ’yanci da burika na bai daya, ya zama wani dandali na nuna girman kan Amurka da ra’ayinta na babakere.

Cikin wani sharhi da aka wallafa a jaridar The Standard ta kasar Kenya da ake fitarwa a kullum, Yirenkyi Jesse ya soki taron, yana mai cewa ya gaza wajen hada kan duniya zuwa ga samun ’yanci da kyakkyawar fata.

Sharhin mai taken “Taro kan demokradiyya na nuna girman kan Amurka” ya kuma ruwaito Yirenkyi Jesse na cewa, taron wanda gwamnatin Biden ta fara a shekarar 2021, ya zama wurin da Amurka ke nuna fuskoki biyu da girman kanta. 

Ya ce ta hanyar amfani da demokradiyya a matsayin makami, Amurka na neman nuna karfinta na babakere, da rarraba kan duniya da kuma kitsa rigingimu.

Daga karshe, Jesse ya bayyana cewa, muddin Amurka ba ta daidaita ayyukanta da furucinta ba, ruhin demokradiyya da take ikirari zai kubce mata, saboda munafurci da girman kai.

Taron karo na 3 zai gudana ne daga yau Litinin zuwa jibi Laraba, a birnin Seol na Korea ta Kudu bisa taken “Demokradiyya Domin Zuri’o’i na Gaba." (Fa’iza Mustapha)