logo

HAUSA

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bukaci jihohin kasar da su samar da cibiyoyin lura da ingantuwar tsaro

2024-03-17 14:45:05 CMG Hausa

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi kira ga gwamnonin jihohin kasar da su samar da cibiyoyin sanya ido da ingantuwar tsaro a makarantun dake jihohinsu domin dakile hare-haren ’yan bindiga da kuma satar dalibai.

Karamin minista a ma’aikatar ilimin kasar Dr. Yusuf Sununu ne ya bukaci hakan lokacin da ya kai ziyarar duba na’urorin zamani da aka samar a babbar cibiyar lura tsaro makarantu ta kasa dake hedikwatar hukumar tsaron al’umma ta Civil Depence a birnin Abuja.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

An dai samar da ita wannan cibiya ce tun a watan Faburairun 2023 da nufin inganta tsaro a makarantu da kuma al’umomin dake suke makwaftaka da makarantun kasar.

Cibiyar wadda take karkashin kulawar hukumar tsaron al’umma ta Civil Depence tana da wakilcin jami’an hukumomin tsaro na kasar, babban aikinta shi ne karbar korafe-karafe da sakonnin da suke bukatar kai daukin gaggawa a duk lokacin da aka samu matsala ta tsaro a cikin makarantun.

Da yake duba kayayyakin, ministan ya yi bayanin cewa, ilimi yana da mahimmancin gaske ga ci gaban kasa, musamman ma idan aka yi la’akari da matakan gina kasa da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bijiro da su. 

“Abun da ya faru a makon da ya gabata, a game da harin da aka kaiwa bangaren ilimi zai iya rage damarmakin da kasarmu ke da shi, a don haka ba za mu dauki wannan al’amari da wasa ba.”

Dr. Yusuf Sununu ya bukaci gwamnonin jihohin kasar da su kara daura damara wajen daukar ingantattun matakai da za su tabbatar da kariya ga makarantu.(Garba Abdullahi Bagwai)