logo

HAUSA

Kwamitin ceton kasa na CNSP ya yi allawadai tare da soke yarjejeniyar soja tare da kasar Amurka

2024-03-17 14:50:24 CMG Hausa

A ranar jiya Asabar 16 ga watan Maris din shekarar 2024, kakakin kwamitin ceton kasa na CNSP kanal Amadou Abdourahamne ya karanto wata sanarwa ta kafofin gwamnatin kasar kan matakin yanke yarjejeniyar soja tare da kasar Amurka.

Daga birnin Yamai, abokin aikimu Mamane Ada ya duba wannan sanarwa ga kuma rahoton da ya aiko mana. 

Sanarwar ta fara da yadda Nijar ta yi allawadai da yarjejeniyar soja da Faransa, da ya kai ga ficewar sojojin Faransa daga kasar Nijar da rufe ofishin jakadancin kasar dake Nijar. Akwai alamun yiyuwar irin haka ya faru bisa la’akari da yadda hukumomin Nijar suka soki yadda kasar Amurka take son yin shisshigi cikin harkokin cikin gida na kasar Nijar, a cewar wannan sanarwa. Da ta fara ambato wata ziyarar tawagar manyan jami’an Amurka a Nijar a makon da ya gabata da ta gana tare da faraminista Ali Mahaman Lamine Zeine. Amma ba tare da ganin shugaban kasa, Abdrouhamane Tiani ba. 

A cewar sanarwar, tawagar ta zo ne domin yin matsin lamba ga sabbin hukumomin soja na su gaggauta dawo da tsarin demokaradiyya tare da gabatar da jadawalin zabe. 

Sai dai a cewar kakakin CNSP kanal Amadou Abdourahamane, ya saida Nijar ga Amurkawa da Faransawa, tare da yarjejeniyar da gwamnatin wancan lokaci ya sanyawa hannu a shekarar 2012, an ci amanar kasar Nijar. Dalilin da kwamitin ceton kasa na CNSP ya dauki wannan mataki tare da cewa shawagin jiragen yaki na Amurka, babban hadari ne ga ’yan Nijar. Shi ya sa, shugaban CNSP birgadiye janar Abdourahamane Tiani, ya dauki wannan mataki mai fa’ida, da yin kira musamman ga ficewar sojojin Amurka dake Nijar, ba tare da bata lokaci ba. Babu wani aikin alheri da suke yi, kuma babu amfanin zamansu a Nijar, in ji kakakin CNSP.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, tun fil’azal kasar Amurka ta zo Nijar ne da muguwar anniya da kuma yaudara, tare da shelantawa duniya cewa suna taimakawa Nijar yaki da ta’addanci. Alhali sojojin Nijar da fararen hula da dama suka mutu duk da makaman da Amurka ta jigbe da sunan yaki da ta’addanci a Nijar, amma kuma ta’addanci sai ci gaba yake, a cewar wannan sanarwa.

 Mamane Ada, sashen Hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar