logo

HAUSA

Kasar Sin Ta Bayyana Matsayarta Kan Batun Kare Hakkin Dan Adam

2024-03-16 15:49:28 CMG Hausa

Jakadan kasar Sin na dindindin a ofishin MDD na Geneva da sauran hukumomin kasa da kasa dake Switzerland, Chen Xu, ya yi wa taro na 55 na majalisar kare hakkin bil Adama ta MDD bayani kan nasarorin da Sin ta samu a bangaren kare hakkin bil adama.

Chen Xu ya ce, kasar Sin ta kasance mai shiga ana damawa da ita cikin harkokin da suka shafi kare hakkokin bil Adama a duniya, haka kuma tana kira ga tattaunawa tsakanin kasa da kasa da hadin gwiwa kan batun, tare da neman daidaito da adalci wajen inganta tabbatar da hakkokin bil Adama daban daban da kuma gaggauta tabbatar da hakkokin samun ci gaban tattalin arziki da zamantakewa da al’adu da daukacin ci gaba.

An amince da kuduri game da tabbatar da hakkokin tattalin arziki da zamantakewa da al’adu, wanda kasashe 80 ciki har da Sin suka gabatar, ba tare da kada kuri’a ba yayin taron majalisar. A cewar Chen Xu, ana kuma fatan wannan kuduri zai taka rawar da ta kamata wajen bayar da gudunmowa ga samun ci gaba mai dorewa. Ya ce, ci gaba da zaman lafiya da kare hakkokin bil Adama, abubuwa ne dake hade da juna kuma masu matukar muhimmanci, yana mai fatan hukumomi daban daban na MDD za su karfafa hadin gwiwa da juna karkashin manufofinsu na aiki. (Fa’iza Mustapha)