logo

HAUSA

Kasar Sin Na Goyon Bayan Kokarin MDD Na Karfafa Gwiwar Mata Da Matasa

2024-03-16 16:57:11 CMG Hausa

Kasar Sin ta bayyana goyon bayanta ga kokarin MDD na karfafawa mata da matasa gwiwa.

Mataimakiyar shugabar kwamitin kula da harkokin yara da mata na majalisar gudanarwar kasar Sin Huang Xiaowei ce ta bayyana hakan a baya-bayan nan, ga wata budaddiyar muhawara ta Kwamitin Sulhu na MDD.

Huang Xiaowei ta kara da cewa, kasar Sin ta kasance mai goyon baya, haka kuma mai aiwatar da ayyukan da suka shafi karfafa gwiwar mata da raya harkokin da suka shafi mata da matasa, kuma Sin ta dukufa wajen ganin mata sun raba moriyar ci gaban tattalin arziki da zamantakewa ta hanyar zartas da dokoki da manufofi da matakai.

Har ila yau, ta ce, kasar Sin ta fitar da sama da mata miliyan 44 na yankunan karkara daga kangin talauci. Kuma yanzu haka, mata ne suka dauki sama da kaso 40 na ma’aikata a kasar, kuma kimanin kaso 45.8 ma’aikata ne a bangaren kimiyya da fasaha, kana kimanin 1 bisa 3n adadin ‘yan kasuwa dake gudanar da sabbin dabarun kasuwanci, kamar cinikayya ta yanar gizo da shirye-shiryen bidiyo na kai tsaye mata ne. (Fa’iza Mustapha)